Zechariah 7:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ كُدَنّٜىٰ مَاتَانْدَ مَذَنْسُ سُكَ مُتُ، كُواْ مَرَايُ، كُواْ وَطَنْدَ بَ یَنْ ڧَسَابَ، كُواْ مَتَلَوْتَ؞ كَدَ وَنِنْكُ يَشِرْيَ وَطَنْعُوَنْسَ مُغُنْتَا أَ ذُوثِيَا؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada kuma ku zalunci gwauruwa, wato wadda mijinta ya rasu, da maraya, da baƙo, da matalauci, kada kuma waninku ya shirya wa ɗan'uwansa mugunta a zuciyarsa.