Zechariah 7:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
‘Na warwatsar da su da guguwa a cikin dukan ƙasashe, inda suka zama baƙi. Aka bar ƙasar ta zama kango bayansu, da har ba mai shiga ko fita. Haka suka sa ƙasan nan mai daɗi ta zama kango.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَا وَرْوَڟَاسُ دَ غُوغُوَ ذُوَا ثِكِنْ أَلْعُمَّنْدَ دَا سُو بَسُ سَنْسُبَ؞ سَبُواْدَ حَكَ سَيْ ڧَسَرْسُ تَذَمَ كُڢَيْ، بَا مَيْ كَيْ دَ كَٰوُاْوَ عَثِكِنْتَ؞ تَهَكَ سُكَ مَيْدَ ڧَسَا مَيْ دَاطِے تَذَمَ كُڢَيْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na sa guguwa ta warwatsa su a cikin al'ummai da ba su san su ba. Ƙasar da suka bari ta zama kango, ba mai kai da kawowa a cikinta. Ƙasa mai kyau ta zama kango.”