Zechariah 9:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana, in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya. Zan tā da ’ya’yanki maza, ya Sihiyona, gāba da ’ya’yanki, ya Girka, in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ لَنْڨُوسَ يَهُودَ كَمَرْ بَكَنَ، ذَنْ كُمَ مَيْدَ إِسْرَٰٓءِيلَ كِبِيَرْسَ؞ ذَنْ تَادَ یَیَ مَظَا نَ سِهِيُواْنَ كَمَرْ تَكُبَ، ذَاسُ ڢَاطَوَ یَیَ مَظَا نَ هٜىٰلَّسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama na tankwasa Yahuza ta zama bakana, Na kuma mai da Ifraimu ta zama kibiya, Zan yi amfani da mutanen Sihiyona kamar takobi, Su yi yaƙi da mutanen Hellas.”