Zechariah 9:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su. Za su hallakar su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa. Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi; za su cika kamar kwanon da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ذَيْ ڟَرٜىٰسُ، ذَاسُ هَلَّكَ أَبُواْكَنْ غَابَا مَاسُ مَجَجَّوَ؞ ذَاسُيِ إِيهٌ نَصَرَا كَمَرْ مَاسُ بُغُوَ، ذَاسُثِكَ كَمَرْ ݣُونُوانْ جِنِنْ بِجِمِنْ هَدَايَ ذَاسُ جِڧُ كَمَرْ ݣُونَرْ بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Mai Runduna zai tsare su, Za su tattake duwatsun majajjawa, Za su sha jini kamar ruwan inabi, Za su cika kamar tasar ruwan inabi, Kamar kuma kusurwoyin bagade.