Zechariah 9:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدُوانْسَ كُمَ عَكَنْ هَمَتْ وَدَّ تَكٜىٰ عَ إِيَاكَرْ دِمَشْڧُ، عِدُوانْسَ يَنَ عَكَنْ تَيَ دَ سِدُوانْ كُواْدَيَكٜىٰ سُنَدَ حِكِمَ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuma yana gāba da Hamat wadda yake kan iyaka, yana kuma gāba da Taya da Sidon ko da yake suna da hikima ƙwarai.