Zechariah 9:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma zan kāre gidana daga sojoji masu kai da kawowa. Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba, gama yanzu ina tsaro.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے ذَنْكُمَ كٜىٰوَيٜىٰ ڧَسَاتَ، إِنْڟَرٜىٰتَ دَغَ سُواْجُواْجِ مَاسُ كَيْ دَ كَٰوُاْوَ، كَدَ مَاسُ دَنِّيَ سُوُثٜىٰ تَڧَسَرْ، غَمَا يَنْذُ عِدَنُونَ عَبُوطٜىٰ سُكٜىٰ عَكَنْ ڧَسَاتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan kafa sansani kewaye da Haikalina saboda maƙiya, Don masu kai da kawowa. Ba wani azzalumi da zai ci su da yaƙi, Gama yanzu ni kaina na gani.”