Zephaniah 1:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ranan nan za tă zama ranar fushi, rana ce ta baƙin ciki da azaba, rana ce ta tashin hankali da lalacewa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
رَانَرْ نَنْ رَانَرْ ڢُشِثٜىٰ، رَانَرْ بَڧِنْ ثِكِ دَ وَهَلَ، رَانَرْ هَلَّكَ دَ ٻَرْنَ، رَانَرْ دُهُ بَڧِ ڧِرِنْ، رَانَرْ غِرْغِجٜىٰ دَ بَڧِنْ دُهُ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan rana ta hasala ce, Ranar azaba da wahala, Ranar lalatarwa da hallakarwa, Ranar duhu baƙi ƙirin, Ranar gizagizai da baƙin duhu,