Zephaniah 2:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Garkuna za su kwanta a can, da kowace irin halitta, Mujiyar hamada da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta. Kukansu za tă ratsa tagogi, ɓuraguzai za su tare ƙofofin shiga, za a kware ginshiƙan al’ul.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَرْكُنَ ذَاسُ ݣُونْتَ أَڟَكِيَرْتَ، دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ نَامَنْ دَاجِ؞ عُنْغُلُ دَ مُجِيَرْ دَاجِ ذَاسُ ذَوْنَ عَكَوُنَنْ غِنْشِڧَنْتَ؞ كُوكَنْ مُجِيَ ذَيْ يِتَڢِتُواْوَ دَغَ تَغَ، نَهَنْكَكَ كُمَ دَغَ بَاكِنْ ڧُواْڢَ؞ كَتَكَنْ سٜىٰدَ نَغِنٜىٰ غِنٜىٰنْتَ، أَبُواْكَنْ غَابَنْتَ ذَاسُ وَرْوَارٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tumaki za su kwanta a tsakiyarta, Da kuma kowace irin dabba ta kowace ƙasa. Mujiya da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta, Ga muryar kuka a taga. Ga risɓewa a bakin ƙofa, Gama za a kware rufin katakan itacen al'ul.