Zephaniah 2:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za tă zama mallakar raguwar gidan Yahuda; a can za su sami wurin kiwo. Da yamma za su kwanta a gidajen Ashkelon. Ubangiji Allahnsu zai lura da su; zai maido musu da martabarsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَاكِنْ تٜىٰكُنْ ذَاتَ ذَمَ وُرِنْ غَادُواْ نَضَغُواْوَرْ غِدَنْ يَهُودَ، وُرِنْ دَ ذَاسُيِ كِيوُاْ؞ أَغِدَاجٜىٰنْ أَشْكٜىٰلُوانْ ذَاسُ ݣُونْتَ إِنْ يَمَّ تَيِ؞ غَمَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسُ ذَيْ كُلَ دَسُو، ذَيْ كُمَ مَيَرْ مُسُ دَ أَلْبَرْكُنْسُ نَدَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gaɓar teku za ta zama ta mutanen Yahuza waɗanda suka ragu, Wurin da za su yi kiwo. Za su kwanta da maraice a gidajen Ashkelon, Gama Ubangiji Allahnsu zai kula da su, Zai kuwa mayar musu da albarkarsu ta dā.