Zephaniah 3:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan rana ba za ku sha kunya saboda laifofin da kuka yi mini, gama zan ɗauke wa wannan birni waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu. Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni a tuduna mai tsarki ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَ رَانَرْ نَنْ بَذَاعَ كُنْيَتَرْ دَكُو بَ، سَبُواْدَ أَيُّكَنْ تَاوَيٜىٰنْ دَ كُنْيِ مِنِ؞ غَمَا ذَنْ ڢِتَرْدَ مَاسُ طَغَ كَيْ دَ مَاسُ تَاڧَمَ دَغَ ثِكِنْكُ؞ بَذَاكُ ڧَارَ طَغَ كَيْ عَبَبَّنْ تُدُنَ مَيْ ڟَرْكِے بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan rana ba za a kunyatar da kai ba, Saboda tayarwar da ka yi mini ta wurin ayyukanka. Gama a sa'an nan zan fitar da masu girmankai Da masu fankama daga cikinka, Ba za ka ƙara yin alfarma ba A dutsena tsattsarka.