Zephaniah 3:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba kya yi wa kowa biyayya, ba kya kuma yarda da kuskurenki. Ba kya dogara ga Ubangiji, ba kya kuma kusatowa kusa da Allahnki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَ كَسَ كُنّٜىٰ غَ كُواْوَ، بَلّٜىٰ مَا يَكَرْٻِ ڠَرَ؞ بَيْ دُواْغَضَ غَ يَهْوٜىٰهْ بَ، بَيْ مَا كُسَنْثِ اللَّهْ نْسَ بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba ya kasa kunne ga muryar kowa, Ba ya karɓar horo. Bai dogara ga Ubangiji ba, Bai kuma kusaci Allahnsa ba.