Zephaniah 3:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan lokaci zan tattara ku; a wannan lokaci zan kawo ku gida, zan sa a yabe ku a kuma girmama ku a cikin dukan mutanen duniya a sa’ad da na maido da arzikinku a idanunku,” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَوَنَّنْ لُواْكَثِ ذَنْ كَٰوُاْكُ غِدَا، أَ لُواْكَثِنْدَ نَتَتَّرَاكُ؞ عِ، ذَنْسَا كُيِ سُونَ كُسَامِ يَبُواْ عَثِكِنْ دُكَنْ ڧَبِيلُنْ دُونِيَا، سَعَدَّ نَمَيَرْ مُكُ دَ أَلْبَرْكُنْكُ كُنَ غَنِ دَ عِدُوانْكُ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan lokaci zan komo da ku gida, In tattara ku wuri ɗaya. Zan sa ku yi suna, Ku sami yabo a wurin mutanen duniya duka, A sa'ad da na mayar muku da arzikinku, Ni Ubangiji na faɗa.”