bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
1 Corinthians 5
1 Corinthians 5
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 4
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 6 →
1
Ana ta cewa akwai fasikanci a tsakaninku, irin wanda ba a yi ko a cikin al'ummai, har wani yana zama da matar ubansa.
2
A! Har kuwa alfarma kuke yi! Ashe, ba gwamma ku yi baƙin ciki ba, har a fitar da wanda ya yi wannan mugun aiki daga cikin jama'arku?
3
Ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan, kamar ma ina nan ne, har ma na riga na yanke wa mutumin da ya yi abin nan hukunci da sunan Ubangijinmu Yesu.
4
Sa'ad da kuka hallara, ruhuna kuma yana nan, da kuma ikon Ubangijinmu Yesu,
5
sai ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don yă hallaka jikinsa, ruhunsa kuma ya tsira a ranar Ubangiji Yesu.
6
Fāriyarku ba shi da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa?
7
Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu.
8
Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.
9
Na rubuta muku a cikin wasiƙata, cewa kada ku yi cuɗanya da fasikai.
10
Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita, da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya.
11
Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.
12
Ina ruwana da hukunta waɗanda ba namu ba? Ba waɗanda suke a cikin Ikkilisiya za ku hukunta ba?
13
Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.
← Chapter 4
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 6 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16