bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
1 Samuel 28
1 Samuel 28
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 29 →
1
A kwanakin nan Filistiyawa suka tattara sojojinsu don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Akish kuwa ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.”
2
Sai Dawuda ya ce, “Za ka ga abin da baranka zai yi.” Akish ya ce wa Dawuda, “Da kyau, zan sa ka cikin zaunannun jarumawan da suke kāre ni.”
3
Sama'ila ya riga ya rasu, dukan Isra'ilawa kuwa suka yi makoki dominsa, suka binne shi a garinsu, wato Rama. Saul kuma ya riga ya kori masu duba da masu maita daga ƙasar.
4
Filistiyawa suka kafa sansaninsu a Shunem. Saul ya tattara Isra'ilawa, su ma suka kafa sansaninsu a Gilbowa.
5
Da Saul ya ga rundunar yaƙin Filistiyawa, sai ya tsorata, ya yi rawar jiki ƙwarai.
6
Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa.
7
Sai ya ce wa barorinsa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.” Barorinsa suka ce masa, “Ai, akwai wata mai duba a Endor.”
8
Sai Saul ya ɓad da kama, ya sa waɗansu tufafi. Shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare. Ya ce mata, “Ina roƙonki ki duba mini ta hanyar sihiri. Ki hawar mini da duk wanda zan faɗa miki.”
9
Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
10
Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”
11
Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?” Ya ce, “Ki hawar mini da Sama'ila.”
12
Da matar ta ga Sama'ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”
13
Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?” Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”
14
Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?” Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.” Saul ya gane Sama'ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.
15
Sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?” Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.”
16
Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?
17
Ai, abin da Ubangiji ya faɗa mini a kanka, shi ne ya cika, gama Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda.
18
Domin ba ka bi maganar Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba, saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau.
19
Banda haka kuma Ubangiji zai ba da Isra'ilawa tare da kai a hannun Filistiyawa. Gobe, da kai da 'ya'yanka maza za ku kasance tare da ni. Ubangiji zai ba da rundunar yaƙin Isra'ila a hannun Filistiyawa.”
20
Da jin maganar Sama'ila sai Saul ya faɗi ƙasa warwar. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome dukan yini da dukan dare ba.
21
Sai matar ta zo wurin Saul, da ta ga ya tsorata, sai ta ce masa, “Baiwarka ta yi kasai da ranta, ta kuwa kasa kunne gare ka.
22
To, kai ma ka kasa kunne ga baiwarka. Bari in ba ka abinci, ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.”
23
Sai ya ƙi, ya ce, “Ba zan ci abinci ba.” Sai da barorinsa da matar suka roƙe shi, sa'an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado.
24
Matar kuwa ta yi hanzari ta yanka turkakken maraƙinta, ta ɗauki gari ta kwaɓa, ta toya abinci marar yisti da shi.
25
Sa'an nan ta kawo wa Saul da barorinsa, suka ci, sa'an nan suka tashi suka tafi da daren nan.
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 29 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31