bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Acts 1
Acts 1
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 2 →
1
Ya Tiyofalas, tarihin nan na farko wanda na rubuta, ya shafi dukan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa,
2
har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.
3
Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah.
4
Sa'ad da yake tare da su, ya umarce su kada su tashi daga Urushalima, amma su jira cikar alkawarin nan da Uba ya yi, “wanda kuka ji daga bakina,
5
domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin 'yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”
6
Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra'ila mulki?”
7
Ya ce musu, “Sanin lokatai da zamanai, da Uba ya sa cikin ikonsa, ba naku ba ne.
8
Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”
9
Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba.
10
Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi.
11
Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”
12
Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da ake kira Dutsen Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya.
13
Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.
14
Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu'a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.
15
To, a kwanakin nan Bitrus ya miƙe tsaye cikin 'yan'uwa, (wajen mutum ɗari da ashirin ne a taron), ya ce,
16
“Ya ku 'yan'uwana, lalle ne a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya faɗa a dā ta bakin Dawuda a game da Yahuza, wanda ya yi wa masu kama Yesu jagaba.
17
Don an lasafta shi cikinmu dā, an kuma ba shi tasa hidima cikin aikin nan.
18
(To, shi mutumin nan, da ladan mugun aikinsa ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kā, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo.
19
Wannan abu fa ya zama sananne ga dukan mazaunan Urushalima, har ake kiran filin Akaldama da harshensu, wato filin jini.)
20
Domin a rubuce yake a Zabura cewa, ‘Gidansa yă zama yasasshe, Kada kowa ya zauna a ciki.’ Da kuma, ‘Matsayinsa wani yă gada.’
21
Don haka, lalle wani daga cikin mutanen nan da suke tare da mu, duk lokacin da Ubangiji Yesu yake cuɗanya da mu,
22
tun daga baftismar da Yahaya ya yi, har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi daga wurinmu aka kai shi zuwa Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.”
23
Sai suka nuna mutum biyu, Yusufu mai suna Barsaba, wanda aka yi wa laƙabi da Yustus, da kuma Matiyas.
24
Sai suka yi addu'a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa,
25
yă karɓi matsayi cikin aikin nan da manzancin nan da Yahuza ya bauɗe wa, don yă cike gurbinsa.”
26
Sai suka yi musu kuri'a, Matiyas ya ci, aka kuma sa shi a cikin manzannin nan goma sha ɗaya.
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 2 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
Recommended Reading
Commentary
Acts Commentaries
→
Devotional
Acts Devotional Guide
→
Get This Bible
Hausa Bible (Littafi Mai Tsarki) Study Bible
→