bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Deuteronomy 20
Deuteronomy 20
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 21 →
1
“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.
2
Sa'ad da kuke gab da kama yaƙi, sai firist ya zo gaba, ya yi magana da jama'a,
3
ya ce musu, ‘Ku ji, ya ku Isra'ilawa, yau kuna gab da kama yaƙi da magabtanku, kada ku karai, ko ku ji tsoro, ko ku yi rawar jiki, ko ku firgita saboda su.
4
Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, zai yaƙi magabtanku dominku, ya ba ku nasara.’
5
“Sa'an nan shugabanni za su yi magana da jama'a, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda ya gina gidan da bai buɗe shi ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya yi bikin buɗewar.
6
Ko akwai wani mutum wanda ya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani wani dabam ya ci amfaninta.
7
Ko akwai wani mutum wanda yake tashin yarinya, amma bai aure ta ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani ya aure ta.’
8
“Shugabannin yaƙi za su ci gaba da yi wa jama'a magana, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda yake jin tsoro, wanda zuciyarsa ta karai? Sai ya koma gidansa don kada ya sa zuciyar sauran 'yan'uwansa kuma su karai.’
9
Sa'ad da shugabannin yaƙi suka daina yi wa jama'a jawabi, sai a zaɓi jarumawan sojoji don su shugabanci mutane.
10
“Sa'ad da kuka kusaci gari don ku yi yaƙi, sai ku fara neman garin da salama.
11
In ya yarda da salamar, har ya buɗe muku ƙofofinsa, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su bauta muku.
12
Amma idan ya ƙi yin salama da ku, amma ya yi yaƙi da ku, sai ku kewaye shi da yaƙi.
13
Idan Ubangiji Allahnku ya bashe shi a hannunku, sai ku karkashe dukan mazaje da takobi.
14
Amma mata, da yara, da dabbobi, da dukan abin da yake cikin garin, da dukan ganimarsa, sai ku kwashe su ganima, ku mori ganimar magabtanku, wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.
15
Haka za ku yi da dukan garuruwan da suke nesa da ku, wato garuruwan da ba na al'umman da suke kusa da ku ba.
16
“Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo.
17
Za ku hallaka su ƙaƙaf, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku,
18
don kada su koya muku yin abubuwa masu banƙyama waɗanda suka yi wa gumakansu, har ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.
19
“Sa'ad da kuka kewaye gari da yaƙi, kuka daɗe kuna yaƙi da shi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari har ku lalata su, gama za ku ci amfaninsu. Kada ku sassare su, gama itatuwan da yake cikin saura ba mutane ba ne, da za ku kewaye su da yaƙi.
20
Sai dai itatuwan da kuka sani ba su ba da 'ya'ya, su ne za ku sassare, ku yi kagara da su saboda garin da kuke yaƙi da shi har ku ci garin.”
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 21 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34