bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Hosea 11
Hosea 11
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 10
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 12 →
1
“A lokacin da Isra'ila yake yaro, na ƙaunace shi, Daga cikin Masar na kirawo ɗana.
2
Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini, Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi, Suna ƙona turare ga gumaka.
3
Ko da yake ni ne na koya wa Ifraimu tafiya. Na ɗauke su a hannuna, Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.
4
Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna, Na zama musu kamar wanda yake ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu. Na sunkuya, na ciyar da su.
5
“Ba su koma ƙasar Masar ba, Amma Assuriya za ta zama sarkinsu Gama sun ƙi yarda su koma wurina.
6
Takobi zai ragargaje biranensu, Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu, Zai cinye su domin muguwar shawararsu.
7
Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da yake an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.
8
“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.
9
Ba zan aikata fushina mai zafi ba, Ba zan ƙara hallaka Ifraimu ba, Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Maitsarki wanda yake tsakiyarku, Ba zan zo wurinku da hasala ba.
10
“Za su bi Ubangiji, Zai yi ruri kamar zaki, hakika zai yi ruri 'Ya'yansa za su zo da rawar jiki da yamma.
11
Da sauri za su zo kamar tsuntsaye daga Masar, Kamar kurciyoyi daga ƙasar Assuriya, Zan komar da su gidajensu, ni Ubangiji na faɗa.”
12
Ubangiji ya ce, “Ifraimu ta kewaye ni da ƙarairayi, Jama'ar Isra'ila kuwa ta kewaye ni da munafuncinta, Yahuza kuma ta tayar wa Allah, Wato tana gāba da Mai Tsarki, mai aminci.
← Chapter 10
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 12 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14