bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Jonah 2
Jonah 2
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 1
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 3 →
1
Sai Yunusa ya yi addu'a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin,
2
ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare ka, ya Ubangiji, Ka a kuwa amsa mini. Daga can cikin lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata.
3
Ka jefa ni cikin zurfi, Can cikin tsakiyar teku, Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni, Kumfa da raƙuman ruwanka suka bi ta kaina.
4
Na ce, an kore ni daga wurinka, Duk da haka zan sāke ganin Haikalinka mai tsarki.
5
Ruwa ya sha kaina, Tekun ta rufe ni ɗungum. Tsire-tsiren teku suka naɗe kaina.
6
Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussan duwatsu. Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada, Amma ka fitar da ni daga cikin ramin, ya Ubangiji Allahna.
7
Sa'ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da kai, ya Ubangiji. Addu'ata kuwa ta kai gare ka a Haikalinka tsattsarka.
8
Su waɗanda suke yin sujada ga gumaka marasa amfani Sun daina yi maka biyayya.
9
Amma ni zan raira yabbai gare ka, Zan miƙa maka sadaka, Zan cika wa'adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.”
10
Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gaɓar teku.
← Chapter 1
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 3 →
All chapters:
1
2
3
4
Recommended Reading
Commentary
Jonah Commentaries
→
Devotional
Jonah Devotional Guide
→
Get This Bible
Hausa Bible (Littafi Mai Tsarki) Study Bible
→