bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Joshua 16
Joshua 16
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 15
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 17 →
1
Rabon zuriyar Yusufu ya milla tun daga Urdun zuwa wajen Yariko, gabas da ruwan Yariko zuwa jejin. Ya haura daga Yariko zuwa ƙasar tuddai zuwa Betel.
2
Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa'an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa.
3
Sai ya gangara yamma zuwa karkarar Yafletiyawa har zuwa karkarar Bet-horon wadda take cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, sa'an nan ya gangara a teku.
4
A nan ne jama'ar Yusufu, wato Manassa da Ifraimu, suka sami nasu gādo.
5
Karkarar jama'ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu.
6
Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta'anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa.
7
Daga Yanowa sai ta gangara zuwa Atarot da Nayaran, ta kuma gegi Yariko, sa'an nan ta gangara a Urdun.
8
Daga Taffuwa, sai iyakar ta yi yamma zuwa rafin Kana, sa'an nan ta gangara a teku. Wannan shi ne gādon Ifraimawa bisa ga iyalansu,
9
tare da garuruwan da ƙauyukan da aka keɓe wa Ifraimawa daga cikin gādon jama'ar Manassa.
10
Amma ba su kori Kan'aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan'aniyawa ka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan'aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole.
← Chapter 15
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 17 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24