bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Leviticus 24
Leviticus 24
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 23
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 25 →
1
Ubangiji kuma ya ce wa Musa
2
ya umarce Isra'ilawa, su kawo masa tsabtataccen man zaitun da aka matse domin fitilar. Fitilar za ta riƙa ci kullum.
3
Za a ajiye ta a gaban labulen shaida a alfarwa ta sujada. Kullum Haruna zai riƙa lura da ita daga maraice har safiya a gaban Ubangiji. Wannan zai zama muku farilla har abada a dukan zamananku.
4
Kullum sai ya shirya fitilun a bisa alkuki na zinariya tsantsa a gaban Ubangiji.
5
Ɗauki lallausan gari a toya gurasa goma sha biyu. A ki kowace gurasa da humushi biyu na garwar gari.
6
A ajiye su bisa tebur na zinariya tsantsa jeri biyu, shida a kowane jeri.
7
Sai a sa lubban tsantsa a kowane jeri don a haɗa da abincin da za a ƙone domin hadaya ta tunawa ga Ubangiji.
8
Kullum a kowace ranar Asabar, Haruna zai kintsa su a gaban Ubangiji domin Isra'ilawa saboda madawwamin alkawarin.
9
Wannan abinci zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza, za su ci a wuri mai tsarki, tun da yake a gare shi rabo ne mai tsarki daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji. Wannan farilla ce har abada.
10
Ɗan wata mace Ba'isra'iliya wanda mahaifinsa Bamasare ne, ya fita, ya yi faɗa da wani Ba'isra'ile a cikin zangon.
11
Sai ɗan Ba'isra'iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwa Shelomit 'yar Dibri na kabilar Dan.
12
Musa kuwa ya kulle shi a gidan tsaro kafin Ubangiji ya faɗa musu abin da za su yi da shi.
13
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
14
“Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama'ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu.
15
Sa'an nan ka faɗa wa Isra'ilawa, cewa, duk wanda ya saɓi Allah zai ɗauki alhakin zunubinsa,
16
za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.
17
“Duk wanda ya kashe mutum, shi ma sai a kashe shi.
18
Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai.
19
“Idan mutum ya yi wa wani rauni, kowane irin rauni ne ya yi masa, shi kuma haka za a yi masa.
20
Idan ya karya masa ƙashi ne, sai a karya nasa ƙashin, idan ya cire wa wani ido, sai a ƙwaƙule nasa, idan haƙori ya ɓalle, sai a ɓalle nasa. Duk irin raunin da ya ji wa wani haka za a yi masa.
21
Wanda ya kashe dabba ya yi ramuwa, wanda kuwa ya kashe mutum sai a kashe shi.
22
Irin shari'ar da za a yi wa baƙo, ita za a yi wa ɗan gari, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”
23
Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.
← Chapter 23
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 25 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27