bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Matthew 28
Matthew 28
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
1
To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun, suka je ganin kabarin.
2
Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala'ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai.
3
Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar dusar ƙanƙara.
4
Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu.
5
Amma sai mala'ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye.
6
Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi.
7
Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa, cewa, ya tashi daga matattu. Ga shi kuma, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. Ga shi, na gaya muku.”
8
Sai suka tashi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farin ciki, suka ruga a guje su kai wa almajiransa labari.
9
Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikun!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.
10
Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa 'yan'uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”
11
Suna tafiya ke nan, sai waɗansu daga cikin sojan nan suka shiga birni, suka ba manyan firistoci labarin da ya auku.
12
Su kuwa da suka taru da shugabannin jama'a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka,
13
suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci.
14
In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen mai mulki, mā rarrashe shi, mu tsare ku daga wahala.”
15
Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan magana kuwa, ta bazu cikin Yahudawa har ya zuwa yau.
16
To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su.
17
Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.
18
Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.
19
Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,
20
kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28