bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Zechariah 13
Zechariah 13
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 12
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 14 →
1
“A ran nan za a buɗe maɓuɓɓuga don wanke zuriyar Dawuda da mazaunan Urushalima daga zunubi da rashin tsarki.
2
A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.
3
Idan har yanzu wani ya ci gaba da yin annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa'an nan mahaifinsa da mahaifiyarsa su soke shi sa'ad da yake annabcin.
4
A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa'ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama'a ba.
5
Amma zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne, ni manomi ne, gama ƙasa abar mallakata ce tun ina yaro.’
6
Idan wani ya tambaye shi cewa, ‘Waɗannan raunukan da suke a hannuwanka fa?’ Zai ce, ‘Ai, raunuka ne da aka yi mini a gidan abokaina.’ ”
7
“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
8
Ni Ubangiji na ce sulusi biyu na ƙasar za su hallaka, Sulusi ɗaya ne kawai zai ragu.
9
Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”
← Chapter 12
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 14 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14