bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
/
Micah 3
Micah 3
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
← Chapter 2
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 4 →
1
Sa’an nan na ce, “Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila. Ya kamata ku san shari’a,
2
ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta, ku da kuke feɗe mutanena kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;
3
ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.”
4
Sa’an nan za su kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa musu ba. A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su saboda irin muguntar da suka yi.
5
Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Game da annabawa masu ɓad da mutanena, in wani ya ciyar da su, sai su ce akwai ‘salama’ amma in bai ciyar da su ba, a shirye suke su kai masa hari.
6
Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba, kuma duhu, ba tare da duba ba. Rana za tă fāɗi wa annabawa, yini kuma zai zama musu duhu.
7
Masu gani za su ji kunya, masu duba kuma za su ji taƙaici. Dukansu za su rufe fuskokinsu gama ba amsa daga Allah.”
8
Amma game da ni, ina cike da iko ta wurin Ruhun Ubangiji da kuma adalci da ƙarfi, don a sanar da Yaƙub laifofinsa, ga Isra’ila kuma zunubinsa.
9
Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila, ku da kuke ƙyamar gaskiya, kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;
10
kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini, Urushalima kuma ta wurin mugunta.
11
Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne, firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su, annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa, “Ba Ubangiji yana tare da mu ba? Ba bala’in da zai zo mana.”
12
Don haka, saboda ku, za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma ta zama tarin juji, tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.
← Chapter 2
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 4 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7