bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
/
Song of Solomon 6
Song of Solomon 6
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
← Chapter 5
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 7 →
1
Ina ƙaunataccenki ya tafi, yake mafiya kyau cikin mata? Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi, don mu taimake ki nemansa.
2
Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, zuwa inda fangulan kayan yaji suke, don yă yi kiwo a cikin lambun don kuma yă tattara furen bi-rana.
3
Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furen bi-rana.
4
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
5
Ki kau da idanu daga gare ni; gama suna rinjayata. Gashinki yana kama da garken awakin da suke gangarawa daga Gileyad.
6
Haƙoranki suna kama da garken tumakin da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
7
Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
8
Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can, da ƙwarƙwarai tamanin da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;
9
amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take, tilo kuwa ga mahaifiyarta, ’yar lele ga wadda ta haife ta. ’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka; sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.
10
Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere?
11
Na gangara zuwa cikin itatuwan almon don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari, don in ga ko inabi sun yi ’ya’ya ko rumman suna fid da furanni.
12
Kafin in san wani abu, sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.
13
Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya; ki dawo, ki dawo, don mu dube ki! Don me kuke duban Bashulammiya sai ka ce rawar Mahanayim?
← Chapter 5
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 7 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8