bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
2 Chronicles 1
2 Chronicles 1
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 2 →
1
Sulemanu ɗan Dawuda ya kahu sosai cikin mulkinsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, Ubangiji kuwa ya sa shi ya zama mashahuri.
2
Sulemanu ya yi magana da dukan manya, wato shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da alƙalai, da dukan shugabanni na Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanni.
3
Sa'an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can.
4
Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.
5
Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama'a suka yi sujada ga Ubangiji a can.
6
Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.
7
A wannan dare Allah ya bayyana ga Sulemanu, ya ce masa, “Ka roƙe ni abin da kake so in ba ka.”
8
Sai Sulemanu ya ce wa Allah, “Ka nuna wa tsohona Dawuda madawwamiyar ƙaunarka, har ka naɗa ni sarki a matsayinsa.
9
Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama'a mai yawa kamar turɓaya.
10
Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”
11
Allah kuwa ya amsa wa Sulemanu ya ce, “Tun da kana da irin wannan tunani a zuciyarka, ba ka kuwa roƙi dukiya, ko wadata, ko girma, ko ran maƙiyanka ba, ba ka kuma roƙi tsawon rai ba, amma ka roƙa wa kanka hikima da sani domin ka iya yin mulkin jama'ata wadda na naɗa ka sarki a kanta,
12
to, na ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka dukiya, da wadata, da girma, waɗanda ba wani sarkin da ya taɓa samun irinsu, ba kuma wani sarkin da zai taɓa samun irinsu.”
13
Daga nan sai Sulemanu ya taso daga masujadar da take Gibeyon inda alfarwa ta sujada take, ya zo Urushalima inda ya zauna yana mulkin Isra'ila.
14
Sai Sulemanu ya tara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), sai ya sa su a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da shi.
15
Sarki ya yawaita azurfa da zinariya har suka zama kamar duwatsu a Urushalima. Haka kuma ya yi da itatuwan al'ul, suka yawaita kamar itatuwan ɓaure a fadama.
16
Wakilan sarki suka ɗauki nauyin shigo da dawakai daga Masar da Kilikiya,
17
suka kuma shigo da karusai daga Masar. Suka riƙa sayar wa sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa karusai a kan azurfa ɗari shida shida, kowane doki kuma a kan azurfa ɗari da hamsin.
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 2 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36