bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
2 Chronicles 28
2 Chronicles 28
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 29 →
1
Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima. Amma shi bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi ba.
2
Ya aikata irin al'amuran da sarakunan Isra'ila suka yi. Ya kuma yi gumakan Ba'al na zubi.
3
Banda haka ma ya ƙona turare a kwarin ɗan Hinnom, ya ƙone 'ya'yansa maza bisa ga ƙazantattun al'adun al'ummai, waɗanda Ubangiji ya kore su daga gaban mutanen Isra'ila.
4
Ya miƙa hadayu, ya ƙona turare a masujadai da a bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.
5
Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya bashe shi a hannun Sarkin Suriya. Suka ci shi da yaƙi suka kama mutanensa da yawa, suka kai su Dimashƙu. Aka kuma bashe shi a hannun Sarkin Isra'ila, wanda ya ci shi da yaƙi, ya kashe masa mutane masu yawa.
6
Gama Feka, ɗan Remaliya, ya kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000) cikin Yahuza a rana ɗaya, dukansu kuwa jarumawa ne, don sun bar bin Ubangiji Allah na kakanninsu.
7
Sai Zikri wani ƙaƙƙarfan mutumin Ifraimu, ya kashe Ma'aseya ɗan sarki, da Azrikam, sarkin fāda, da Elkana wanda yake daga sarki sai shi.
8
Mutanen Isra'ila kuwa suka kwaso 'yan'uwansu da suka kama, mutum dubu ɗari biyu (200,000), mata, da 'ya'ya mata, da 'ya'ya maza. Suka kuma kwaso ganima mai yawan gaske daga gare su. Suka kawo ganimar a Samariya.
9
Amma wani annabin Ubangiji yana nan, sunansa Oded. Shi wannan annabi ya tafi ya taryi rundunar da ta zo Samariya, ya ce musu, “Ga shi, saboda Ubangiji Allah na kakanninku ya yi fushi da Yahuza, ya bashe su a hannunku, ku kuka kashe su da zafin fushi wanda ya kai har sama.
10
Yanzu kuwa kuna niyya ku mai da jama'ar Yahuza da ta Urushalima su zama bayinku mata da maza. Ashe, ku kanku ba ku da waɗansu zunuban da kuka yi wa Ubangiji Allahnku?
11
Yanzu fa, sai ku saurare ni, ku mayar da kamammun da kuka kwaso daga 'yan'uwanku gama Ubangiji yana fushi da ku ƙwarai.”
12
Waɗansu daga cikin shugabannin 'ya'ya maza na Ifraimu, wato su Azariya ɗan Yohenan, da Berikiya ɗan Meshillemot, da Yehizkiya ɗan Shallum, da Amasa ɗan Hadlai suka tashi suka tsayar da masu komowa daga wurin yaƙin.
13
Suka ce musu, “Kada ku shigo nan da waɗanda kuka kamo daga wurin yaƙin, gama so kuke ku jawo mana laifi a gaban Ubangiji, a kan manyan zunuban da muka riga muka yi, gama Ubangiji yana fushi da Isra'ila ƙwarai.”
14
Don haka sai sojoji suka bar waɗanda suka kamo daga wurin yaƙi, da ganima a gaban sarakuna da dukan taron.
15
Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin 'yan'uwansu a Yariko, wato birnin itatuwan dabino, sa'an nan suka koma Samariya.
16
A wannan lokaci kuwa sarki Ahaz ya nemi taimako wurin sarakunan Assuriya.
17
Gama Edomawa suka sāke kai wa Yahuza yaƙi, suka kama mutane suka tafi da su.
18
Filistiyawa kuma sun kai hari a biranen ƙasar Shefela, da Negeb ta Yahuza, har suka ci Bet-shemesh, da Ayalon, da Gederot, da Soko da ƙauyukanta, da Timna da ƙauyukanta, da Gimzo da ƙauyukanta. Sai suka zauna a can.
19
Ubangiji kuwa ya ƙasƙantar da Yahuza, saboda Ahaz Sarkin Yahuza ya yi ganganci a Yahuza, ya zama marar aminci ga Ubangiji.
20
Sai Tiglatfilesar, Sarkin Assuriya, ya zo ya yi yaƙi da shi, ya wahalshe shi, maimakon ya taimake shi.
21
Sai Ahaz ya kwaso kaya daga Haikalin Ubangiji, da fādar sarki, da na sarakuna, ya ba Sarkin Assuriya, amma sam, bai taimake shi ba.
22
Duk da wannan wahala da sarki Ahaz yake sha a wannan lokaci, sai ƙara rashin aminci yake yi ga Ubangiji.
23
Gama ya miƙa hadaya ga gumakan Dimashƙu, ga waɗanda suka ci shi da yaƙi, ya ce, “Saboda gumakan sarakunan Suriya sun taimake su, ni ma zan miƙa musu hadaya don su taimake ni.” Amma suka zama masa dalilin lalacewa, shi da dukan Isra'ila.
24
Sai Ahaz kuma ya tattara tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya farfashe su. Ya kuma kukkulle ƙofofin Haikalin Ubangiji, ya gina wa kansa bagadai a kowane lungu na Urushalima.
25
A kowane birni na Yahuza, ya yi masujadai inda zai ƙona turare ga gumaka, ya sa Ubangiji, Allah na kakanninsa ya yi fushi.
26
Sauran ayyukansa da dukan al'amuransa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila.
27
Ahaz ya rasu, suka binne shi cikin birnin Urushalima, amma ba su kai shi hurumin sarakunan Isra'ila ba. Hezekiya ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 29 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36