bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Amos 1
Amos 1
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 2 →
1
Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
2
Amos ya ce, “Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona, Muryarsa za ta yi tsawa daga Urushalima. Da jin wannan, sai wuraren kiwo za su bushe, Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yake kore zai yi yaushi.”
3
Ubangiji ya ce, “Mutanen Dimashƙu sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun zalunci mutanen Gileyad da zalunci mai tsanani.
4
Don haka zan aukar da wuta a kan fādar Sarkin Suriya. Za ta ƙone kagarar Ben-hadad, sarki.
5
Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofin birnin Dimashƙu, In kawar da masu sarautar Bet-eden da na kwarin Awen. Za a kwashe mutanen Suriya ganima zuwa ƙasar Kir.”
6
Ubangiji ya ce, “Mutanen Gaza sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun kwashe al'umma duka, sun sayar wa mutanen Edom.
7
Saboda haka zan aukar da wuta a kan garun Gaza ta ƙone kagarar birnin.
8
Zan kawar da masu sarautar biranen Ashdod da Ashkelon, Zan karɓe sandan mulkin Ekron. Sauran Filistiyawa da suka ragu kuma, Za su mutu duka.”
9
Ubangiji ya ce, “Mutanen Taya sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun kwashe mutanen sun kai ƙasar Edom. Suka karya yarjejeniyar abuta wadda suka yi.
10
Saboda haka zan aukar da wuta a kan garun Taya, Ta ƙone kagarar birnin.”
11
Ubangiji ya ce, “Mutanen Edom sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun farauci 'yan'uwansu, Isra'ilawa, Suka ƙi su nuna musu jinƙai. Ba su yarda su huce daga fushinsu ba.
12
Saboda haka zan aukar da wuta a kan Teman, Ta ƙone kagarar Bozara.”
13
Ubangiji ya ce, “Mutanen Ammon sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don haɗamarsu ta ƙasa, Suka tsaga mata masu ciki a Gileyad.
14
Saboda haka zan aukar da wuta a kan garun Rabba, Ta ƙone kagarar birnin. Za a yi kururuwa a ranar yaƙi, Faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.
15
Sarkinsu da manyan mutanensu za a kai su wata ƙasa dabam.”
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 2 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9