bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Amos 3
Amos 3
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 2
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 4 →
1
Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.
2
Daga cikin dukan al'umman da nake ƙauna a duniya, Ku kaɗai ne na sani, Nake kuma kulawa da ku, Don haka zan hukunta ku saboda zunubanku.”
3
Zai yiwu a ce mutum biyu za su yi tafiya tare, Amma su rasa shirya magana?
4
Zai yiwu zaki yă yi ruri a jeji Ba tare da ya kama nama ba? Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani a kogonsa In bai kama wani abu ba?
5
Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasa In ba a kafa masa tarko ba? Zai yiwu tarko ya zargu In bai kama wani abu ne ba?
6
Zai yiwu mutane su rasa firgita, Idan aka busa ƙahon yaƙi a birni? Zai yiwu wata babbar masifa ta auko wa birni Ba da yardar Ubangiji ba?
7
Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.
8
Zaki ya yi ruri! Wa ba zai ji tsoro ba? Sa'ad da Ubangiji ya yi magana! Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?
9
Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”
10
Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.
11
“Saboda haka abokan gaba za su kewaye ƙasarsu, Su hallakar da kagaransu, Su washe gidajen nan nasu masu daraja.”
12
Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci ƙafafu biyu Ko kunne ɗaya na tunkiya daga bakin zaki, Haka nan kuma kima daga cikin mutanen Samariya Waɗanda suke zaman jin daɗi za su tsira.
13
Ku saurara yanzu, Ku yi wa zuriyar Yakubu kashedi,” In ji Ubangiji, Maɗaukaki.
14
“Ran da na hukunta mutanen Isra'ila saboda zunubansu, Zan hallakar da bagadan Betel. Za a kakkarya zankayen bagaden, Su fāɗi ƙasa.
15
Zan murmushe gidajensu na rani da na damuna. Zan hallakar da gidajen da aka ƙawata da hauren giwa, Kowane babban gida kuwa za a rushe shi.”
← Chapter 2
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 4 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9