bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Numbers 17
Numbers 17
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 16
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 18 →
1
Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,
2
“Ka faɗa wa Isra'ilawa su ba ka sanduna, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Ka rubuta sunan kowane mutum a sandansa.
3
Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lawi, gama akwai sanda guda domin kowane gidan kakanninsu.
4
Sai ka ajiye su a alfarwa ta sujada a gaban akwatin alkawari, inda nakan sadu da kai.
5
Mutumin da sandansa ya yi toho, shi ne na zaɓa, da haka zan sa gunagunin da Isra'ilawa suke yi a kaina ya ƙare.”
6
Musa kuwa ya yi magana da Isra'ilawa. Sai dukan shugabanninsu suka ba shi sanda ɗaya ɗaya, sanda ɗaya daga kowane shugaba bisa ga gidajen kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Sandan Haruna yana cikin sandunan.
7
Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji cikin alfarwa ta sujada.
8
Kashegari Musa ya shiga alfarwar, sai ga shi, sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya huda, ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi 'ya'yan almon nunannu, wato wani irin itace ne mai kama da na yazawa.
9
Musa kuwa ya fito wa Isra'ilawa da dukan sandunan da aka ajiye a gaban Ubangiji. Suka duba, kowanne ya ɗauki sandansa.
10
Ubangiji ya ce wa Musa, “Mayar da sandan Haruna a akwatin alkawari, alama ce ga masu tawaye ta cewa za su mutu idan ba su daina gunaguninsu ba.”
11
Haka kuwa Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi.
12
Isra'ilawa suka ce wa Musa, “Ba shakka, mun hallaka. Mun lalace, dukanmu mun lalace.
13
Duk wanda ya kusaci alfarwa ta sujada ta Ubangiji, zai mutu. Ashe, dukanmu za mu mutu ke nan!”
← Chapter 16
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 18 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36