bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Numbers 9
Numbers 9
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 8
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 10 →
1
Sai Ubangiji ya yi wa Musa magana a jejin Sinai a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar, ya ce,
2
“Sai Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokacinsa.
3
A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka'idodinsa duka.”
4
Musa kuwa ya faɗa wa Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa.
5
Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sinai bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.
6
Akwai waɗansu mutane da suka ƙazantu ta wurin taɓa gawar wani mutum,don haka ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a ranar ba. Sai suka zo wurin Musa da Haruna a ranar,
7
suka ce masa, “Ai, mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa. Me ya sa aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran 'yan'uwanmu a ƙayyadadden lokacin yinta?”
8
Sai Musa ya ce musu, “Dakata, har na ji abin da Ubangiji zai umarta a kanku.”
9
Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa
10
ya faɗa wa Isra'ilawa ya ce, “Idan wani mutum na cikinku, ko na cikin zuriyarku, ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji.
11
Za su kiyaye shi da maraice a watan biyu yana da kwana goma sha huɗu. Za su ci shi da abinci marar yisti da ganyaye masu ɗaci.
12
Kada su bar kome daga cikinsa ya kai gobe, kada kuwa a fasa ƙashinsa, sai su yi shi bisa ga dukan umarnin Idin Ƙetarewa.
13
Amma mutumin da yake da tsarki, bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi kiyaye Idin Ƙetarewa, sai a raba wannan mutum da jama'arsa, gama bai miƙa hadayar Ubangiji a ƙayyadadden lokacin yinta ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.
14
“Idan baƙo yana zaune a wurinku, shi ma sai ya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji bisa ga umarnai da ka'idodi na Idin Ƙetarewa. Ka'ida ɗaya ce ga baƙo da ɗan gari.”
15
A ranar da aka kafa alfarwa ta sujada, sai girgije ya sauko ya rufe ta. Da maraice kuwa girgijen yana kamar wuta.
17
A duk lokacin da aka gusar da girgijen, sai Isra'ilawa su kama hanya. A inda girgijen ya tsaya, nan kuma Isra'ilawa za su kafa zango.
18
Da umarnin Ubangiji Isra'ilawa suke tashi, da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana bisa alfarwar, sukan yi ta zamansu a zangon.
19
Ko da girgije ya daɗe a bisa alfarwar Isra'ilawa ba sukan tashi ba, sukan bi umarnin Ubangiji.
20
Wani lokaci girgijen yakan yi 'yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji.
21
Wani lokaci girgijen yakan zauna a bisa alfarwar daga maraice zuwa safiya ne kawai, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. Amma idan girgijen ya yini, ya kwana, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi.
22
Ko kwana biyu ne girgijen ya yi, yana zaune a bisa alfarwar ko wata guda, ko fi, sai Isra'ilawa su yi ta zamansu a zangon, ba za su tashi ba. Amma in ya tashi, sai su kuma su tashi.
23
Da umarnin Ubangiji suke sauka, da umarninsa kuma suke tashi, suna bin faɗarsa, yadda ya umarci Musa.
← Chapter 8
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 10 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36