bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Revelation 10
Revelation 10
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 9
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 11 →
1
Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.
2
Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,
3
ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki yana ruri. Da ya yi kiran, sai aradun nan bakwai suka yi tsawa.
4
Sa'ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.”
5
Sai mala'ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama,
6
ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma,
7
sai dai a lokacin busa ƙahon da mala'ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.
8
Sa'an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala'ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.”
9
Sai na je wurin mala'ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.”
10
Sai na karɓi ƙaramin littafin daga hannun mala'ikan, na cinye. Sai ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma da na cinye, cikina ya ɗau ɗaci.
11
Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sāke yin annabci a game da jama'a iri iri, da al'ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”
← Chapter 9
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 11 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22