bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Revelation 15
Revelation 15
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 14
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 16 →
1
Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala'iku bakwai masu bala'i bakwai, waɗanda suke bala'in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.
2
Sai na ga wani abu kamar bahar na gilas, gauraye da wuta, na kuma ga waɗanda suka yi nasara da dabbar nan, da siffarta, da kuma lambar sunanta, a tsaitsaye a bakin bahar na gilas, da molayen yabon Allah a hannunsu.
3
Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa, “Ayyukanka manya ne, masu banmamaki, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki! Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma, Ya Sarkin al'ummai.
4
Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, Ya kuma ɗaukaka sunanka? Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki. Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada, Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”
5
Bayan wannan na duba, ga Wuri Mafi Tsarki a buɗe a Haikali a Sama.
6
Sai mala'ika bakwai ɗin nan masu bala'i bakwai suka fito daga Haikalin, saye da tufafin lilin mai tsabta, mai ɗaukar iko, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.
7
Sai ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan guda huɗu, ta ba mala'ikun nan bakwai tasoshi bakwai na zinariya, a cike da fushin Allah, shi da yake a raye har abada abadin.
8
Sai Haikalin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga ɗaukakar Allah da ikonsa. Ba mai iya shiga Haikalin nan, sai bayan bala'i bakwai na mala'ikun nan bakwai sun ƙare.
← Chapter 14
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 16 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22