bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Revelation 8
Revelation 8
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 7
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 9 →
1
Sa'ad da Ɗan Ragon ya ɓamɓare hatimi na bakwai, aka yi shiru a Sama kamar na rabin sa'a.
2
Sa'an nan na ga mala'ikun nan bakwai da suke a tsaye a gaban Allah, an ba su ƙaho bakwai.
3
Ga kuma wani mala'ika ya zo ya tsaya a gaban bagadin ƙona turare, riƙe da tasar zinariya ta turaren ƙonawa. Sai aka ba shi turare mai yawa, domin ya haɗa da addu'o'in tsarkaka duka a kan bagadin ƙona turare na zinariya a gaban kursiyin.
4
Sai hayaƙin turaren ya tashi daga hannun mala'ikan tare da addu'o'in tsarkaka, ya isa a gaban Allah.
5
Sai mala'ikan ya ɗauki tasar nan ta turaren ƙonawa, ya cika ta da wuta daga bagadin ƙona turare, ya watsa a kan duniya, sai aka yi ta aradu, da ƙararraki masu tsanani, da walƙiya, da kuma rawar ƙasa.
6
Sa'an nan mala'ikun nan bakwai masu ƙaho bakwai ɗin nan, suka yi shirin busa su.
7
Mala'ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
8
Mala'ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. Sulusin teku ya zama jini,
9
sulusin halittar da suke a ruwa suka mutu, sulusin jiragen ruwa kuma suka hallaka.
10
Mala'ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro ya faɗo daga sama, yana cin wuta kamar cukwima. Ya faɗa a sulusin koguna da maɓuɓɓugan ruwa.
11
Sunan tauraron kuwa Ɗaci. Sulusin ruwa ya zama mai ɗaci, sai mutane da yawa suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.
12
Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.
13
Sa'an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala'ikun nan uku suke shirin busawa!”
← Chapter 7
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 9 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22