bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Exodus 13
Exodus 13
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 12
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 14 →
1
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Keɓe mini 'ya'yan fari maza duka. Kowane ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa cikin Isra'ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”
3
Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.
4
A wannan rana kuka fita, wato a watan Abib.
5
Sai ku kiyaye wannan farilla a wannan wata sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, wadda ya rantse wa kakanninku zai ba ku, wato ƙasar da take ba da yalwar abinci.
6
Sai ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai, amma a rana ta bakwai za ku yi idi ga Ubangiji.
7
Abinci marar yisti za a ci har kwana bakwai. Kada a ga wani da abinci mai yisti, ko kuma yisti ɗin kansa, a ko'ina a wurarenku.
8
A wannan rana kowa zai sanar wa ɗansa cewa abubuwan nan da muke yi, muna yi ne don tunawa da abin da Ubangiji ya yi mana sa'ad da ya fitar da mu daga Masar.
9
Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.
10
Sai ku kiyaye farillan nan kowace shekara a lokacinta.”
11
“Sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa wadda zai ba ku kamar yadda ya rantse muku, ku da kakanninku,
12
sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Kowane ɗan farin dabbarku na Ubangiji ne.
13
Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. Idan kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Kowane ɗan farin 'ya'yanku, sai ku fanshe shi.
14
In wata rana 'ya'yanku suka tambaye ku cewa, ‘Ina ma'anar wannan?’ Sai ku ce musu, ‘Da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar, daga gidan bauta.
15
Gama sa'ad da Fir'auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan 'ya'yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da 'ya'yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan 'ya'yan farinmu, maza.’
16
Al'amarin nan kuwa zai zama matuni kamar alama a hannunku ko a goshinku, gama da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar.”
17
Da Fir'auna ya bar jama'a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, “Don kada jama'a su sāke tunaninsu sa'ad da suka ga yaƙi, su koma Masar.”
18
Amma Allah ya kewaya da jama'a ta hanyar jeji, wajen Bahar Maliya. Isra'ilawa kuwa suka fita daga ƙasar Masar da shirin yaƙi.
19
Musa ya kuma ɗauki ƙasusuwan Yusufu, gama Yusufu ya riga ya rantsar da Isra'ilawa su kwashe ƙasusuwansa daga Masar sa'ad da Allah ya ziyarce su.
20
Sai suka ci gaba da tafiya daga Sukkot suka yi zango a Etam a gefen jejin.
21
Da rana Ubangiji yakan yi musu jagora da al'amudin girgije, da dare kuwa da al'amudin wuta, domin ya ba su haske domin su iya tafiya dare da rana.
22
Al'amudan nan biyu kuwa, na girgijen da na wutar, ba su daina yi wa jama'a jagora ba.
← Chapter 12
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 14 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40