bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Exodus 6
Exodus 6
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 5
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 7 →
1
Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”
2
Allah kuma ya yi magana da Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji.
3
Na bayyana ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a kan ni Allah Maɗaukaki ne, amma sunan nan nawa, Yahweh, ban sanasshe su ba.
4
Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan'ana, inda suka yi zaman baƙunci.
5
Yanzu na ji nishin Isra'ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuwa tuna da alkawarina.
6
Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.
7
Zan tallafe ku, ku zama jama'ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya 'yanto ku daga wulakancin Masarawa.
8
Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.”’
9
Sai Musa ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne gare shi ba, saboda ɓacin rai da tsananin bauta.
10
Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
11
“Tafi gaban Fir'auna, Sarkin Masar, ka faɗa masa ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa.”
12
Amma Musa ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Duba, tun da yake Isra'ilawa ba su kasa kunne gare ni ba, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni, ni mutum mai nauyin baki?”
13
Ubangiji kuma ya yi magana da Musa da Haruna, su tafi wurin Isra'ilawa da wurin Fir'auna, Sarkin Masar, su ba su umarni, su kuma fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar.
14
Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu.
15
'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan Bakan'aniya, waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.
16
Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. Lawi ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.
17
'Ya'yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu.
18
'Ya'ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku.
19
'Ya'ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu.
20
Amram ya auri Yokabed 'yar'uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.
21
'Ya'yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri.
22
'Ya'ya maza na Uzziyel, su ne Mishayel, da Elzafan, da Zitri.
23
Haruna ya auri Elisheba, 'yar Amminadab 'yar'uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.
24
'Ya'ya maza na Kora, su ne Assir, da Elkana, da Abiyasaf. Waɗannan su ne iyalin Kora.
25
Ele'azara, ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin 'ya'ya mata na Futiyel. Ita kuwa ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan kabilar Lawi bisa ga kabilansu.
26
Wannan Haruna ne da Musa, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana su fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar, ƙungiya ƙungiya.
27
Su ne waɗanda suka yi magana da Sarkin Masar ya bar Isra'ilawa su fita daga Masar. Musa da Haruna ne suka yi wannan.
28
Wata rana Ubangiji ya yi magana da Musa a ƙasar Masar ya ce,
29
“Ni ne Ubangiji, sai ka faɗa wa Fir'auna, Sarkin Masar, dukan abin da na faɗa maka.”
30
Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni?”
← Chapter 5
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 7 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40