bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Exodus 27
Exodus 27
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 26
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 28 →
1
“Za ku yi bagaden da itacen ƙirya, mai tsawo kamu biyar, da fāɗi kamu biyar, tsayinsa kamu uku. Bagaden zai zama murabba'i.
2
A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla.
3
Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.
4
Za ku kuma yi wa bagaden raga da tagulla, sa'an nan ku sa wa ragar ƙawane a kusurwoyinta huɗu.
5
Za ku sa ragar a cikin bagaden a tsakiya.
6
Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da tagulla.
7
Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa.
8
Za ku yi bagaden da katakai, sa'an nan ku roɓe cikinsa. Ku yi shi bisa ga fasalin da na nuna maka bisa dutsen.
9
“Za ku yi wa alfarwa farfajiya. A kudancin farfajiyar, sai ku rataye labule mai tsawo kamu ɗari wanda aka saƙa da lallausan zaren lilin.
10
Za ku yi masa dirkoki guda ashirin, da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.
11
A wajen arewa kuma, sai ku rataya labule mai tsawon kamu ɗari. Ku yi masa dirkoki da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.
12
Fāɗin labulen a wajen yamma na farfajiyar, zai zama kamu hamsin. A yi wa labulen dirkoki goma, a kuma yi wa dirkokin kwasfa goma.
13
Fāɗin labulen wajen gabas na farfajiyar zai zama kamu hamsin.
14
Labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.
15
Haka kuma labulen ƙofa na wancan gefe zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.
16
Za a saƙa labule mai kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai launi shuɗi, da shunayya, da mulufi domin ƙofar farfajiyar. Za a sa wa ƙofar dirkoki huɗu tare da kwasfansu huɗu.
17
Za a yi wa dukan dirkokin da suke kewaye da farfajiyar maɗaurai da maratayai na azurfa, da kwasfa ta tagulla.
18
Tsawon farfajiyar zai zama kamu ɗari, fāɗinta kamu hamsin, tsayinta kamu biyar. Za a saƙa labulenta da lallausan zaren lilin, a kuma yi kwasfanta da tagulla.
19
Da tagulla kuma za a yi turakun alfarwar, da turakun farfajiyar, da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a cikin alfarwar.”
20
“Sai a umarci Isra'ilawa su kawo tsabtataccen man zaitun tatacce domin fitilar. Za a kunna fitilar ta yi ta ci koyaushe.
21
Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da 'ya'yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka'ida har abada ga Isra'ilawa.”
← Chapter 26
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 28 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40