bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Exodus 33
Exodus 33
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 32
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 34 →
1
Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi, ka kama hanya, kai da jama'ar da ka fisshe su daga ƙasar Masar, zuwa ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, na ce, ‘Ga zuriyarka zan ba da ita.’
2
Zan kuwa aiki mala'ika a gabanka. Zan kuma kori Kan'aniyawa da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Farizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.
3
Ka kama hanya zuwa ƙasa mai yalwar abinci, amma fa ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurin kai, domin kada in hallaka ku a hanya.”
4
Da jama'ar suka ji wannan mugun labari, sai suka yi nadama. Ba wanda ya sa kayan ado.
5
Gama Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurin kai. In na yi tafiya tare da ku, nan da nan zan hallaka ku. Domin haka fa, yanzu, ku tuɓe kayan adonku, domin in san abin da zan yi da ku.”’
6
Domin haka Isra'ilawa suka tuɓe kayan adonsu tun daga dutsen Horeb har zuwa gaba.
7
Musa ya ɗauki alfarwa, ya kafa ta a bayan zango, nesa da zango. Ya kuwa sa mata suna, Alfarwa ta Sujada. Duk wanda yake neman Ubangiji, sai ya tafi alfarwa ta sujada, wanda yake a bayan zango.
8
Duk sa'ad da Musa ya tafi wurin alfarwar, jama'a duka sukan tashi tsaye, kowa ya tsaya a ƙofar alfarwarsa, ya kallaci Musa, har ya shiga alfarwar.
9
Sa'ad da Musa ya shiga alfarwar, al'amudin girgije ya sauko ya tsaya bisa ƙofar alfarwar, Ubangiji kuma ya yi magana da Musa.
10
A sa'ad da jama'a suka ga al'amudin girgijen nan na tsaye a ƙofar alfarwar, sai jama'ar duka su tashi su yi sujada, kowa a ƙofar alfarwarsa.
11
Ta haka Ubangiji ya riƙa yin magana da Musa baki da baki, kamar yadda mutum yakan yi magana da amininsa. Sa'ad da Musa ya koma cikin zango kuma, baransa, Joshuwa, ɗan Num, saurayi, ba zai fita daga cikin alfarwar ba.
12
Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’
13
Yanzu ina roƙonka idan na sami tagomashi a gare ka, ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma sami tagomashi a wurinka, ka kuma tuna, wannan al'umma jama'arka ce.”
14
Ubangiji kuwa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.”
15
Musa kuwa ya ce masa, “In ba za ka tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan.
16
Yaya zan sani ko na sami tagomashi a wurinka, ni da jama'arka, in ba ka tafi tare da mu ba? Yaya ni da jama'arka, za a bambanta mu da sauran jama'ar da suke a duniya?”
17
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka ce, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”
18
Musa kuwa ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini kanka.”
19
Sai Ubangiji ya ce masa, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda nā yi wa alheri, in nuna jinƙai ga wanda nā yi wa jinƙai.”
20
Ya kuma ce, “Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama mutum ba zai gan ni ba, ya rayu.”
21
Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen.
22
A sa'ad da zatina yake wucewa, zan sa ka a tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har in wuce,
23
sa'an nan in ɗauke hannuna, za ka kuwa ga bayana, amma ba za ka ga fuskata ba.”
← Chapter 32
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 34 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40