bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Psalms 107
Psalms 107
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 106
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Chapter 122
Chapter 123
Chapter 124
Chapter 125
Chapter 126
Chapter 127
Chapter 128
Chapter 129
Chapter 130
Chapter 131
Chapter 132
Chapter 133
Chapter 134
Chapter 135
Chapter 136
Chapter 137
Chapter 138
Chapter 139
Chapter 140
Chapter 141
Chapter 142
Chapter 143
Chapter 144
Chapter 145
Chapter 146
Chapter 147
Chapter 148
Chapter 149
Chapter 150
Chapter 108 →
1
Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce!
2
Ku zo mu yabi Ubangiji tare, Dukanku waɗanda ya fansa, Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.
3
Ya komo da ku daga ƙasashen waje, Daga gabas da yamma, kudu da arewa.
4
Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya, Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.
5
Suka yi ta fama da yunwa, da ƙishirwa, Suka fid da zuciya ga kome.
6
Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
7
Ya fisshe su, ya bi da su sosai, Zuwa birnin da za su zauna.
8
Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu!
9
Ya shayar da waɗanda suke jin ƙishirwa, Ya kuma ƙosar da mayunwata da alheransa.
10
Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa, 'Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,
11
Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki, Sun kuwa ƙi koyarwarsa.
12
Suka gaji tiƙis saboda tsananin aiki, Za su faɗi ƙasa, ba mataimaki.
13
A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
14
Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa, Ya tsintsinka sarƙoƙinsu.
15
Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
16
Ya kakkarya ƙofofin da aka yi da tagulla. Ya kuma ragargaza ƙyamaren da aka yi da baƙin ƙarfe.
17
Waɗansu suka yi ciwo sabili da zunubansu, Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.
18
Ba su so su ga abinci, Sun kusa mutuwa.
19
A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.
20
Da umarninsa ya warkar da su, Ya cece su daga kabari.
21
Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
22
Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu, Su raira waƙoƙin murna, Su faɗi dukan abin da ya yi!
23
Waɗansu suka yi tafiya a teku da jirage, Suna samun abin zaman garinsu daga tekuna.
24
Suka ga abin da Ubangiji ya aikata, Ayyukansa masu banmamaki waɗanda ya yi a tekuna.
25
Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi, Ta fara hurowa, ta sa raƙuman ruwa su tashi.
26
Aka ɗaga jiragen ruwa sama, Sa'an nan suka tsinduma cikin zurfafa. Da mutanen suka ga irin hatsarin da suke ciki, Sai zuciyarsu ta karai.
27
Suka yi ta tuntuɓe suna ta tangaɗi kamar bugaggu, Gwanintarsu duka ta zama ta banza.
28
Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabarsu.
29
Ya sa hadiri ya yi tsit, Raƙuman ruwa kuma suka yi shiru.
30
Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru, Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya, Wurin da suke so.
31
Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
32
Dole su yi shelar girmansa cikin taron jama'a, Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.
33
Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf, Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.
34
Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani, Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.
35
Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa, Ya kuma mai da busasshiyar ƙasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.
36
Ya bar mayunwata su zauna a can, Suka kuwa gina birni don su zauna a ciki.
37
Suka shuka gonaki suka dasa kurangar inabi, Waɗanda suka ba da amfani mai yawan gaske.
38
Ya sa wa jama'arsa albarka, Suka kuwa haifi 'ya'ya da yawa. Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.
39
Sa'ad da aka ci nasara a kan jama'ar Allah, Aka ƙasƙantar da su ta wurin mugun zalunci, Da wahalar da aka yi musu.
40
Sai Allah ya wulakanta waɗanda suka zalunci jama'arsa. Ya sa su suka yi ta kai da kawowa A hamada inda ba hanya.
41
Ya tsamo masu bukata daga cikin baƙin cikinsu, Ya sa iyalansu su riɓaɓɓanya kamar garkunan tumaki.
42
Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna, Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.
43
Da ma a ce masu hikima Za su yi tunani a kan waɗannan abubuwa, Da ma kuma su yarda Da madawwamiyar ƙaunar Ubangiji.
← Chapter 106
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Chapter 122
Chapter 123
Chapter 124
Chapter 125
Chapter 126
Chapter 127
Chapter 128
Chapter 129
Chapter 130
Chapter 131
Chapter 132
Chapter 133
Chapter 134
Chapter 135
Chapter 136
Chapter 137
Chapter 138
Chapter 139
Chapter 140
Chapter 141
Chapter 142
Chapter 143
Chapter 144
Chapter 145
Chapter 146
Chapter 147
Chapter 148
Chapter 149
Chapter 150
Chapter 108 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
67
68
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
91
92
93
94
95
96
97
98
99
100
101
102
103
104
105
106
107
108
109
110
111
112
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
134
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150