bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Psalms 119
Psalms 119
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 118
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Chapter 122
Chapter 123
Chapter 124
Chapter 125
Chapter 126
Chapter 127
Chapter 128
Chapter 129
Chapter 130
Chapter 131
Chapter 132
Chapter 133
Chapter 134
Chapter 135
Chapter 136
Chapter 137
Chapter 138
Chapter 139
Chapter 140
Chapter 141
Chapter 142
Chapter 143
Chapter 144
Chapter 145
Chapter 146
Chapter 147
Chapter 148
Chapter 149
Chapter 150
Chapter 120 →
1
Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu, Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.
2
Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa, Waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.
3
Hakika ba su yin laifi, Sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji.
4
Kai ka ba mu dokokinka, Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.
5
Na sa zuciya zan yi aminci, Game da kiyaye dokokinka!
6
Idan na kula da dukan umarnanka, To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.
7
Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya, A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.
8
Zan yi biyayya da dokokinka, Ko kusa kada ka kashe ni!
9
Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki? Sai ta wurin biyayya da umarnanka.
10
Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka, Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!
11
Na riƙe maganarka a zuciyata, Don kada in yi maka zunubi.
12
Ina yabonka, Ya Ubangiji, Ka koya mini ka'idodinka!
13
Zan ta da murya, In maimaita dukan dokokin da ka bayar.
14
Ina murna da bin umarnanka, Fiye da samun dukiya mai yawa.
15
Nakan yi nazarin umarnanka, Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.
16
Ina murna da dokokinka, Ba zan manta da umarnanka ba.
17
Ka yi mini alheri, ni bawanka, Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.
18
Ka buɗe idona Domin in ga gaskiyar shari'arka mai banmamaki.
19
Zamana a nan duniya na ɗan lokaci kaɗan ne. Kada ka ɓoye mini umarnanka!
20
Zuciyata ta ƙosa saboda marmari, A kowane lokaci ina so in san hukuntanka.
21
Kakan tsauta wa masu girmankai, La'anannu ne waɗanda suka ƙi bin umarnanka.
22
Ka kuɓutar da ni daga cin mutuncinsu da raininsu, Domin na kiyaye dokokinka.
23
Ko da sarakuna za su taru Su shirya mini maƙarƙashiya, Duka da haka, ni bawanka, Zan yi nazarin ka'idodinka.
24
Umarnanka suna faranta mini rai, Su ne mashawartana.
25
Ina kwance cikin ƙura, an yi nasara da ni, Ka wartsakar da ni kamar yadda ka alkawarta!
26
Na hurta dukan abin da na aikata, ka kuwa amsa mini, Ka koya mini ka'idodinka!
27
Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka, In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.
28
Ɓacin rai ya ci ƙarfina, Ka ƙarfafa ni, kamar yadda ka alkawarta.
29
Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya, Ta wurin alherinka, ka koya mini dokarka.
30
Na yi niyya in yi biyayya, Na mai da hankali ga ka'idodinka.
31
Na bi umarnanka, ya Ubangiji, Kada ka sa in kasa ci wa burina!
32
Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka, Gama za ka ƙara mini fahimi.
33
Ka koya mini ma'anar dokokinka, ya Ubangiji, Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci.
34
Ka fassara mini dokarka, ni kuwa zan yi biyayya da ita, Zan kiyaye ta da zuciya ɗaya.
35
Ka bishe ni a hanyar umarnanka, Domin a cikinsu nakan sami farin ciki
36
Ka sa ni in so yin biyayya da ka'idodinka, Fiye da samun dukiya.
37
Ka kiyaye ni daga mai da hankali ga abin da yake marar amfani, Ka yi mini alheri kamar yadda ka alkawarta.
38
Ka tabbatar da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka, Irin wanda kakan yi wa waɗanda suke tsoronka.
39
Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro, Ka'idodinka suna da amfani ƙwarai!
40
Ina so in yi biyayya da umarnanka, Gama kai mai adalci ne, Ka yi mini alheri!
41
Ka nuna mini yawan ƙaunar da kake yi mini, ya Ubangiji, Ka cece ni bisa ga alkawarinka.
42
Sa'an nan zan amsa wa waɗanda suke cin mutuncina, Domin na dogara ga maganarka.
43
Ka ba ni iko in iyar da saƙonka na gaskiya a kowane lokaci, Gama sa zuciyata tana ga hukuntanka.
44
Kullum zan yi biyayya da dokarka har abada abadin!
45
Zan rayu da cikakken 'yanci, Gama na yi ƙoƙari in kiyaye ka'idodinka.
46
Zan hurta umarnanka ga sarakuna, Ba kuwa zan ji kunya ba.
47
Ina murna in yi biyayya da umarnanka, Saboda in ƙaunarsu.
48
Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu, Zan yi ta tunani a kan koyarwarka.
49
Ka tuna da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka, Ka ƙarfafa zuciyata.
50
Ko ina shan wahala, ana ta'azantar da ni, Saboda alkawarinka yana rayar da ni.
51
Masu girmankai suna raina ni, Amma ban rabu da dokarka ba.
52
Na tuna da koyarwar da ka yi mini a dā, Sukan kuwa ta'azantar da ni, ya Ubangiji.
53
Haushi ya kama ni sosai, Sa'ad da na ga mugaye suna keta dokarka.
54
Ina zaune can nesa da gidana na ainihi, Sai na ƙago waƙoƙi a kan umarnanka.
55
Da dare nakan tuna da kai, ya Ubangiji, Ina kuwa kiyaye dokarka.
56
Wannan shi ne farin cikina, In yi biyayya da umarnanka.
57
Kai kaɗai nake so, ya Ubangiji, Na yi alkawari in yi biyayya da dokokinka.
58
Ina roƙonka da zuciya ɗaya, Ka yi mini jinƙai kamar yadda ka alkawarta!
59
Na yi tunani a kan ayyukana, Na yi alkawari in bi ka'idodinka.
60
Ba tare da ɓata lokaci ba, Zan gaggauta in kiyaye umarnanka.
61
Mugaye sun ɗaure ni tam da igiyoyi, Amma ba zan manta da dokarka ba.
62
Da tsakar dare nakan farka, In yabe ka saboda hukuntanka masu adalci.
63
Ina abuta da duk waɗanda suke bauta maka, Da duk waɗanda suke kiyaye dokokinka.
64
Ya Ubangiji, duniya ta cika da madawwamiyar ƙaunarka, Ka koya mini umarnanka!
65
Kana cika alkawarinka, ya Ubangiji, Kana kuwa yi mini alheri, ni bawanka.
66
Ka ba ni hikima da ilimi Domin ina dogara ga umarnanka.
67
Kafin ka hore ni nakan yi kuskure, Amma yanzu ina biyayya da maganarka.
68
Managarci ne kai, mai alheri ne kuma, Ka koya mini umarnanka!
69
Masu girmankai sun faɗi ƙarairayi a kaina, Amma da zuciya ɗaya nake biyayya da ka'idodinka.
70
Waɗannan mutane ba su da ganewa, Amma ni ina murna da dokarka.
71
Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarnanka.
72
Dokar da ka yi Muhimmiya ce a gare ni, Fiye da dukan dukiyar duniya.
73
Kai ne ka halicce ni, ka kuma kiyaye ni lafiya, Ka ba ni ganewa, don in koyi dokokinka.
74
Waɗanda suke tsoronka za su yi murna sa'ad da suka gan ni, Saboda ina dogara ga alkawarinka.
75
Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji, Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.
76
Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta ta'azantar da ni, Kamar yadda ka alkawarta mini, ni bawanka.
77
Ka yi mini jinƙai, zan rayu, Saboda ina murna da dokarka.
78
Ka kunyatar da masu girmankai Saboda sun ba da shaidar zur a kaina, Amma ni, zan yi tunani a kan ka'idodinka.
79
Ka sa waɗanda suke tsoronka su zo gare ni, Da waɗanda suka san umarnanka.
80
Ka sa in yi cikakkiyar biyayya da umarnanka, Sa'an nan zan tsere wa shan kunyar faɗuwa.
81
Na tafke, ya Ubangiji, jira nake ka cece ni, Na dogara ga maganarka.
82
Idanuna sun gaji da zuba ido ga alkawarinka. Roƙo nake, “Sai yaushe za ka taimake ni?”
83
Na zama marar amfani kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita, Duk da haka ban manta da umarnanka ba.
84
Har yaushe zan yi ta jira? Yaushe za ka yi wa waɗanda suke tsananta mini hukunci?
85
Masu girmankai, waɗanda ba su biyayya da dokarka, Sun haƙa wushefe don su kama ni.
86
Umarnanka duka, abin dogara ne, Mutane suna tsananta mini da ƙarairayi, Ka taimake ni!
87
Sun kusa ci wa burinsu na su kashe ni, Amma ban raina ka'idodinka ba.
88
Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri, Domin in yi biyayya da dokokinka.
89
Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji, A kafe take a Sama.
90
Amincinka ya tabbata har abada, Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin.
91
Dukan abubuwa suna nan har wa yau saboda umarninka, Domin su duka bayinka ne.
92
Da ba domin dokarka ita ce sanadin farin cikina ba, Da na mutu saboda hukuncin da na sha.
93
Faufau ba zan raina ka'idodinka ba, Gama saboda su ka bar ni da rai.
94
Ni naka ne, ka cece ni! Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.
95
Mugaye suna jira su kashe ni, Amma zan yi ta tunani a kan dokokinka.
96
Na koya cewa ba wani abu da yake cikakke, Amma umarninka ba shi da iyaka.
97
Ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina ta tunani a kanta dukan yini.
98
Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci, Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.
99
Ganewata ta fi ta dukan malamaina, Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.
100
Na fi tsofaffi hikima, Saboda ina biyayya da umarnanka.
101
Nakan guje wa halin mugunta Saboda ina so in yi biyayya da maganarka.
102
Ban raina koyarwarka ba Saboda kai ne ka koya mini.
103
Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi, Har sun fi zuma zaƙi!
104
Na ƙaru da hikima daga dokokinka, Saboda haka ina ƙin dukan halin da yake ba daidai ba.
105
Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni, Haske ne kuma a kan hanyata.
106
Zan cika muhimmin alkawarina, In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.
107
Azabaina, ya Ubangiji, suna da yawa, Ka rayar da ni kamar yadda ka alkawarta!
108
Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji, Ka koya mini umarnanka.
109
Kullum a shirye nake in kasai da raina, Ban manta da umarninka ba.
110
Mugaye sun kafa mini tarko, Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.
111
Umarnanka nawa ne har abada, Su ne murnar zuciyata.
112
Na ƙudura zan yi biyayya da ka'idodinka, Har ranar mutuwata.
113
Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci, Amma ina ƙaunar dokarka.
114
Kai ne kake kāre ni, kake kuma kiyaye ni, Ina sa zuciya ga alkawarinka.
115
Ku rabu da ni, ku masu zunubi! Zan yi biyayya da umarnan Allahna.
116
Ka ƙarfafa ni kamar yadda ka alkawarta, zan kuwa rayu, Kada ka bar ni in kasa ci wa burina!
117
Ka riƙe ni, sai in zauna lafiya, Koyaushe zan mai da hankali ga umarnanka.
118
Ka rabu da dukan waɗanda ba su biyayya da dokokinka, Dabarunsu na yaudara banza ne.
119
Kakan yi banza da duk mai mugunta, Don haka ina ƙaunar koyarwarka.
120
Saboda kai, nake jin tsoro, Na cika da tsoro saboda shari'unka.
121
Na yi abin da yake daidai mai kyau, Kada ka bar ni a hannun maƙiyana!
122
Sai ka yi alkawari za ka taimaki bawanka, Kada ka bar masu girmankai su wahalshe ni!
123
Idanuna sun gaji da duban hanyar cetonka, Ceton da ka alkawarta.
124
Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka, Ka koya mini umarnanka.
125
Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa, Don in san koyarwarka.
126
Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu, Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!
127
Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya, Fiye da zinariya tsantsa.
128
Saboda haka ina bin dukan koyarwarka, Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.
129
Koyarwarka tana da ban al'ajabi, Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.
130
Fassarar koyarwarka takan ba da haske, Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.
131
Ina haki da baki a buɗe, Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.
132
Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai, Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.
133
Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta, Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.
134
Ka cece ni daga waɗanda suke zaluntata, Domin in yi biyayya da umarnanka.
135
Ka sa mini albarka da kasancewarka tare da ni, Ka koya mini dokokinka.
136
Hawayena suna malalowa kamar kogi, Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.
137
Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, Dokokinka kuma daidai ne,
138
Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne, Daidai ne kuwa.
139
Fushi yana cina kamar wuta, Saboda maƙiyana ba su kula da umarnanka ba.
140
Alkawarinka ba ya tashi! Bawanka yana ƙaunar alkawarinka ƙwarai!
141
Ni ba kome ba ne, rainanne ne, Amma ban ƙi kula da ka'idodinka ba.
142
Adalcinka zai tabbata har abada, Dokarka gaskiya ce koyaushe.
143
A cike nake da wahala da damuwa, Amma umarnanka suna faranta zuciyata.
144
Koyarwarka masu adalci ne har abada, Ka ba ni ganewa domin in rayu.
145
Ina kira gare ka da zuciya ɗaya, Ka amsa mini, ya Ubangiji, Zan yi biyayya da umarnanka!
146
Ina kira gare ka, Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!
147
Tun kafin fitowar rana ina kira gare ka neman taimako, Na sa zuciya ga alkawarinka.
148
Dare farai ban yi barci ba, Ina ta bimbini a kan koyarwarka.
149
Ka ji ni, ya Ubangiji, bisa ga madawwamiyar ƙaunarka, Ka kiyaye raina bisa ga alherinka!
150
Mugayen nan waɗanda suke tsananta mini sun matso kusa, Mutanen da ba su taɓa kiyaye dokarka ba.
151
Amma kana kusa da ni, ya Ubangiji, Dukan alkawaranka gaskiya ne.
152
Tuntuni na ji labarin koyarwarka, Ka sa su tabbata har abada.
153
Ka dubi wahalata, ka cece ni, Gama ban ƙi kulawa da dokarka ba.
154
Ka kāre manufata, ka kuɓutar da ni, Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
155
Ba za a ceci mugaye ba, Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.
156
Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji, Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.
157
Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa, Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.
158
Sa'ad da na dubi waɗannan maciya amana, Sai in ji ƙyama ƙwarai, Domin ba su yi biyayya da umarninka ba.
159
Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji! Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.
160
Cibiyar dokarka gaskiya ce, Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.
161
Ƙarfafan mutane sun auka mini ba dalili, Amma maganarka ce nake girmamawa.
162
In farin ciki ƙwarai saboda alkawaranka, Farin cikina kamar na wanda ya sami dukiya mai yawa ne.
163
Ina ƙin ƙarairayi, ba na jin daɗinsu, Amma ina ƙaunar dokarka.
164
A kowace rana nakan gode maka sau bakwai, Saboda shari'unka masu adalci ne.
165
Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya, Ba wani abin da zai sa su fāɗi.
166
Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji, Ina aikata abin da ka umarta.
167
Ina biyayya da ka'idodinka, Ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.
168
Ina biyayya da umarnanka da koyarwarka, Kana kuwa ganin dukan abin da nake yi.
169
Bari kukana yă kai gare ka, ya Ubangiji! Ka ganar da ni kamar yadda ka alkawarta.
170
Bari addu'ata ta zo gare ka, Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
171
Zan yabe ka kullayaumin Domin ka koya mini ka'idodinka.
172
Zan raira waƙa a kan alkawarinka, Domin umarnanka a gaskiya ne.
173
Kullum a shirye kake domin ka taimake ni, Saboda ina bin umarnanka.
174
Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji! Ina samun farin ciki ga dokarka.
175
Ka rayar da ni don in yabe ka, Ka sa koyarwarka su taimake ni!
176
Ina kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya, Ka zo ka neme ni, ni bawanka, Saboda ban ƙi kulawa da dokokinka ba.
← Chapter 118
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Chapter 122
Chapter 123
Chapter 124
Chapter 125
Chapter 126
Chapter 127
Chapter 128
Chapter 129
Chapter 130
Chapter 131
Chapter 132
Chapter 133
Chapter 134
Chapter 135
Chapter 136
Chapter 137
Chapter 138
Chapter 139
Chapter 140
Chapter 141
Chapter 142
Chapter 143
Chapter 144
Chapter 145
Chapter 146
Chapter 147
Chapter 148
Chapter 149
Chapter 150
Chapter 120 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
67
68
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
91
92
93
94
95
96
97
98
99
100
101
102
103
104
105
106
107
108
109
110
111
112
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
134
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150