bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Psalms 69
Psalms 69
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 68
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Chapter 122
Chapter 123
Chapter 124
Chapter 125
Chapter 126
Chapter 127
Chapter 128
Chapter 129
Chapter 130
Chapter 131
Chapter 132
Chapter 133
Chapter 134
Chapter 135
Chapter 136
Chapter 137
Chapter 138
Chapter 139
Chapter 140
Chapter 141
Chapter 142
Chapter 143
Chapter 144
Chapter 145
Chapter 146
Chapter 147
Chapter 148
Chapter 149
Chapter 150
Chapter 70 →
1
Ka cece ni, ya Allah! Ruwa ya sha kaina.
2
Ina nutsewa cikin laka mai zurfi, Ba kuwa ƙasa mai ƙarfi, Na tsunduma cikin ruwa mai zurfi, Raƙuman ruwa kuwa sun kusa kashe ni.
3
Na gaji da kira, ina neman taimako, Maƙogwarona yana yi mini ciwo, Idanuna duka sun gaji, Saboda ina zuba ido ga taimakonka.
4
Waɗanda suke ƙina ba dalili Sun fi gashin kaina yawa, Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina, Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni. Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.
5
Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah, Ka san irin wawancin da na yi!
6
Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka, Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka! Kada ka bar ni in jawo abin kunya Ga waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!
7
Sabili da kai ne aka ci mutuncina, Kunya ta rufe ni.
8
Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana, Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.
9
Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a Haikalinka Tana iza ni a ciki kamar wuta, Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.
10
Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi, Jama'a kuwa suka ci mutuncina.
11
Na sa tufafin makoki, Sai suka maishe ni abin dariya.
12
A tituna suna ta magana a kaina, Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.
13
Amma ni, zan yi addu'a gare ka, ya Ubangiji, Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa, Sabili da muhimmiyar ƙaunarka, Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.
14
Ka cece ni daga nutsewa cikin wannan laka, Ka kiyaye ni daga maƙiyana, Daga kuma wannan ruwa mai zurfi.
15
Kada ka bar ambaliyar ruwa ta rufe ni. Kada ka bar ni in mutu cikin zurfafa, Ko in nutse a cikin kabari.
16
Sabili da madawwamiyar ƙaunarka, ka amsa mini, ya Ubangiji, Ka juyo wurina, saboda juyayinka mai girma!
17
Kada ka ɓoye kanka daga bawanka, Ina shan babbar wahala, ka yi hanzari ka amsa mini!
18
Ka zo ka fanshe ni, Ka kuɓutar da ni daga abokan gābana.
19
Ka san yadda ake cin mutuncina, Da yadda ake kunyata ni, ake ƙasƙantar da ni, Kana ganin dukan abokan gābana.
20
Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini, Ni kuwa ba ni da mataimaki, Na sa zuciya za a kula da ni, Amma babu. Na sa zuciya zan sami ta'aziyya, Amma ban samu ba.
21
Sa'ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi, Sa'ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.
22
Allah ya sa bukukuwansu su zama lalacewarsu, Shagulgulansu kuma su zama sanadin fāɗuwarsu!
23
Ka makantar da su, har da ba za su iya gani ba, Kullum ka sa bayansu ya ƙage!
24
Ka kwarara musu fushinka, Bari zafin fushinka ya ci musu!
25
Allah ya sa su gudu su bar sansaninsu, Kada wani ya ragu da rai cikin alfarwansu!
26
Sun tsananta wa waɗanda ka hukunta, Suna taɗin shan wuyar waɗanda ka aukar wa cutar.
27
Ka riɓaɓɓanya zunubansu, Kada ka bar su su sami rabon kome daga cikin cetonka.
28
Ka sa a goge sunansu daga cikin littafin rai, Kada a sa su a lissafin jama'arka.
29
Amma ni mai bukata ne, ina shan wahala, Ka tsame ni, ya Allah, ka cece ni!
30
Zan raira waƙar yabo ga Allah, Zan yi shelar girmansa ta wurin yi masa godiya,
31
Wannan zai daɗaɗa wa Ubangiji rai Fiye da hadayar bijimi, Fiye da a ba shi bijimi bana bakwai.
32
Sa'ad da masu bukata suka ga wannan za su yi murna, Waɗanda suke yi wa Allah sujada kuwa za a ƙarfafa su.
33
Ubangiji yana kasa kunne ga masu bukata, Bai manta da jama'arsa da suke a kurkuku ba.
34
Ku yabi Allah, ku al'arshi da duniya, ku yabi Allah, Tekuna da dukan talikan da suke cikinsu!
35
Gama zai ceci Sihiyona, Ya sāke gina garuruwan Yahuza, Jama'arsa za su zauna a wurin, su mallaki ƙasar.
36
Zuriyar bayinsa za su gāje ta, Masu ƙaunarsa za su zauna a wurin.
← Chapter 68
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Chapter 122
Chapter 123
Chapter 124
Chapter 125
Chapter 126
Chapter 127
Chapter 128
Chapter 129
Chapter 130
Chapter 131
Chapter 132
Chapter 133
Chapter 134
Chapter 135
Chapter 136
Chapter 137
Chapter 138
Chapter 139
Chapter 140
Chapter 141
Chapter 142
Chapter 143
Chapter 144
Chapter 145
Chapter 146
Chapter 147
Chapter 148
Chapter 149
Chapter 150
Chapter 70 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
67
68
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
91
92
93
94
95
96
97
98
99
100
101
102
103
104
105
106
107
108
109
110
111
112
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
134
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150