bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
1 Chronicles 10
1 Chronicles 10
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 9
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 11 →
1
Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ilawa, Isra'ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa.
2
Filistiyawa suka kama Saul da 'ya'yansa maza, suka kashe Jonatan da Yishwi, da Malkishuwa.
3
Yaƙin ya tsananta wa Saul, maharba suka rutsa Saul, suka yi masa rauni.
4
Sai Saul ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Zare takobinka, ka kashe ni, don kada marasa kaciyan nan su zo su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar makamai nasa bai yarda ba, gama yana jin tsoro ƙwarai. Saboda haka sai Saul ya zare takobinsa ya fāɗi a kansa.
5
Sa'ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, sai shi ma ya faɗi a kan takobinsa ya mutu.
6
Ta haka Saul ya mutu, shi da 'ya'yansa maza guda uku tare da dukan gidansa.
7
Sa'ad da dukan Isra'ilawa waɗanda suke zaune a kwari suka ga sojojin sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa suka zo suka zauna a wurin.
8
Kashegari, sa'ad da Filistiyawa suka tafi su kwashe waɗanda aka kashe, sai suka tarar da Saul da 'ya'yansa maza matattu a Dutsen Gilbowa.
9
Suka kuwa tuɓe tufafinsa, suka datse kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka aiki manzanni ko'ina a ƙasar Filistiyawa don su ba gumakansu da jama'arsu wannan albishir.
10
Sai suka ajiye kayan yaƙin Saul a gidan gumakansu, suka kuma rataye kansa a gidan gunkin nan, wato Dagon.
11
Sa'ad da mutanen Yabesh-gileyad suka ji irin abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,
12
sai dukan ƙarfafan mutanensu suka tafi suka ɗauki gawar Saul, da gawawwakin 'ya'yansa, suka kawo a Yabesh suka binne ƙasusuwansu a ƙarƙashin itacen oak cikin Yabesh. Suka yi azumi har kwana bakwai.
13
Haka nan Saul ya mutu saboda laifin da ya yi wa Ubangiji, gama bai kiyaye maganar Ubangiji ba, saboda kuma ya nemi shawara wurin masu mabiya.
14
Amma bai nemi Ubangiji ba. Domin haka Ubangiji ya kashe shi, ya ɗauki sarautar, ya ba Dawuda ɗan Yesse.
← Chapter 9
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 11 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29