bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
1 Chronicles 14
1 Chronicles 14
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 13
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 15 →
1
Sai Hiram Sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda, su kai masa itatuwan al'ul, da magina, da massassaƙa domin a gina masa fāda.
2
Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya tabbatar masa da sarautar Isra'ila, mulkinsa kuwa ya ɗaukaka ƙwarai saboda jama'arsa, Isra'ila.
3
Dawuda kuwa ya ƙara auren waɗansu mata a Urushalima, suka haifi 'ya'ya mata da maza.
4
Ga sunayen 'ya'yan da aka haifa masa a Urushalima, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,
5
da Ibhar, da Elishuwa, da Elifelet,
6
da Noga, da Nefeg, da Yafiya,
7
da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.
8
Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka, sai dukan Filistiyawa suka haura, suna neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya fita domin ya yi yaƙi da su.
9
Filistiyawa suka iso kwarin Refayawa suka fara fatali da shi.
10
Sai Dawuda ya roƙi Allah, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya amsa masa, ya ce, “Ka haura, gama zan bashe su a hannunka.”
11
Sai suka haura zuwa Ba'al-ferazim, Dawuda kuwa ya ci su da yaƙi a wurin. Sai ya ce, “Allah ya raraki maƙiyana ta hannuna, kamar yadda ruwa yakan rarake ƙasa.” Don haka aka sa wa wurin suna Ba'al-ferazim.
12
Filistiyawa suka gudu suka bar gumakansu a wurin. Dawuda kuwa ya yi umarni, aka ƙone su duka.
13
Filistiyawa kuma suka sāke kawo yaƙi a kwarin.
14
Dawuda ya sāke yin roƙo ga Allah, Allah kuwa ya ce masa, “Kada ka hau zuwa wurinsu, ka kewaye ka ɓullo musu ta baya daura da itatuwan tsamiya.
15
Sa'ad da ka ji motsi kamar na tafiyar sojoji a bisa itatuwan tsamiya, sai ka fita ka yi yaƙi, gama Allah ya wuce ta gabanka don ya bugi sojojin Filistiyawa.”
16
Dawuda fa ya yi daidai yadda Ubangiji ya umarce shi. Suka bugi sojojin Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.
17
Sunan Dawuda kuma ya kai ko'ina cikin dukan ƙasashe. Ubangiji kuwa ya sa dukan al'ummai su ji tsoron Dawuda.
← Chapter 13
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 15 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29