bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
1 Chronicles 20
1 Chronicles 20
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 21 →
1
Da bazara, lokacin da sarakuna sukan fita su yi yaƙi, sai Yowab ya tafi da sojoji suka lalatar da ƙasar Ammonawa. Suka tafi, suka kewaye Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima. Yowab ya bugi Rabba ya yi nasara da ita.
2
Sai Dawuda ya ciro kambi daga kan sarkinsu, sai ya iske nauyinsa talanti ɗaya na zinariya ne, akwai kuma duwatsu masu daraja a cikinsa. Dawuda ya sa kambin a kansa. Ya kwaso ganima da yawa a birnin.
3
Ya kuma fito da mutanen da suke ciki, ya yanyanka su da zartuna da makamai masu kaifi, da gatura. Haka Dawuda ya yi wa dukan biranen Ammonawa. Sa'an nan Dawuda da dukan jama'a suka koma Urushalima.
4
Bayan wannan kuma, sai yaƙi ya tashi a Gat tsakanin Isra'ilawa da Filistiyawa, sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar ƙattin nan. Aka ci Filistiyawa.
5
Yaƙi kuma ya sake tashi tsakanin Isra'ilawa da Filistiyawa, sai Elhanan ɗan Yayir, ya kashe Lahmi ɗan'uwan Goliyat daga Gat, wanda yake gorar mashinsa ta yi ya dirkar masaƙa.
6
Yaƙi ya sāke tashi a Gat, inda wani cindo, ƙaton mutum yake. Yana da yatsotsi ashirin da huɗu, wato a kowane hannu yana da yatsa shida, haka nan kuma a kowace ƙafarsa. Shi kuma daga zuriyar ƙattin nan ne.
7
Sa'ad da ya yi wa mutanen Isra'ila ba'a, sai Jonatan ɗan Shimeya, wato ɗan'uwan Dawuda, ya kashe shi.
8
Waɗannan uku ne Dawuda da jama'arsa suka kashe daga zuriyar ƙattin na Gat.
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 21 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29