bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Proverbs 17
Proverbs 17
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 16
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 18 →
1
Gara a ci ƙanzo da rai a kwance, da gida cike da liyafa, amma cike da tashin hankali.
2
Bara mai wayo yakan sami iko a kan shashashan ɗan maigidansa, har ya sami rabo a cikin gādon.
3
Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.
4
Mugaye sukan kasa kunne ga mugayen dabaru, maƙaryata kuma sukan kasa kunne ga ƙarairayi.
5
Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.
6
Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza.
7
Mutumin da yake kamili ba ya faɗar ƙarya, haka ma wawa ba zai faɗi wani abin kirki ba.
8
Waɗansu mutane suna tsammani cin rashawa yakan yi aiki kamar sihiri, sun gaskata zai iya yin kome.
9
Idan kana so mutane su so ka, ka riƙa yafe musu sa'ad da suka yi maka laifi. Mita takan raba abuta.
10
Mutum mai fasaha yakan koyi abu da yawa daga tsautawa ɗaya, fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.
11
Mutuwa za ta zo wa mugaye kamar mugun manzo wanda a ko yaushe yana so ya kuta tashin hankali.
12
Gara mutum ya gamu da beyar ta mata wadda aka kwashe mata kwiyakwiyanta, da ka gamu da waɗansu wawaye suna aikin dakikancinsu.
13
Idan ka sāka alheri da mugunta, ba za ka iya raba gidanka da mugunta ba, faufau.
14
Mafarin jayayya kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta haɓaka ba.
15
Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.
16
Kashe kuɗi saboda ilimi ba shi da amfanin kome ga wawa, domin ba shi da tunani.
17
A ko yaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, 'yan'uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.
18
Sai mutum marar tunani ne kaɗai zai ɗauki lamunin basusuwan maƙwabcinsa.
19
Shi wanda yake son zunubi, yana son wahala ke nan, wanda kuma yake yin fāriya a dukan lokaci yana neman tashin hankali ke nan.
20
Mutumin da yakan yi tunanin mugunta, ya kuma hurta ta, kada ya sa zuciya ga samun abin kirki, sai dai bala'i kaɗai.
21
Mahaifi wanda ɗansa yake yin abubuwan wauta, ba shi da kome sai ɓacin rai da baƙin ciki.
22
Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya. Zama da baƙin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.
23
Alƙalai marasa gaskiya suna cin hanci a ɓoye, sa'an nan ba za su aikata adalci ba.
24
Baligi da hikima yake aikinsa, amma wanda bai balaga ba, bai san abin da zai yi ba.
25
Wawan da yakan jawo wa mahaifinsa ɓacin rai, abin baƙin ciki yake ga mahaifiyarsa.
26
Ba daidai ba ne a ci marar laifi tara, yi wa mutumin kirki bulala kuwa rashin adalci ne.
27
Mutumin da ya tabbata yana da gaskiya ba zai cika yawan magana ba, natsattsen mutum yana da basira ƙwarai.
28
Banda haka ma, ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, mai basira.
← Chapter 16
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 18 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31