bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Proverbs 29
Proverbs 29
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 28
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 30 →
1
Wanda ake ta tsauta wa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta ƙare farat ɗaya.
2
Sa'ad da masu adalci suke mulki, jama'a sukan yi murna, amma sa'ad da mugaye suke mulki, jama'a sukan yi nishi.
3
Wanda yake ƙaunar hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa. Amma wanda yake abuta da karuwai zai lalatar da dukiyarsa.
4
Sarkin da yake aikata adalci ƙasarsa za ta yi ƙarƙo, amma wanda yake karɓar rashawa zai lalatar da ƙasar.
5
Mutum wanda yake yi wa maƙwabcinsa daɗin baƙi yana kafa wa kansa tarko.
6
Laifin mugun zai zama tarko a gare shi, amma adali zai raira waƙa, ya yi farin ciki.
7
Adali yana sane da hakkin matalauta, amma mugun bai san wannan ba.
8
Ashararai sukan sa wa birni wuta, amma masu hikima sukan kwantar da hasala.
9
Idan gardama ta shiga tsakanin mai hikima da wawa, sai wawa ya yi ta fushi, ko kuwa ya yi ta dariya, gardamar dai ba za ta ƙare ba.
10
Mutane masu kisankai suna ƙin amintaccen mutum, amma adalai za su kiyaye ransa.
11
Wawa yakan nuna fushinsa ko yaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa.
12
Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun ƙarya, dukan ma'aikatansa za su zama maƙaryata.
13
Matalauci da azzalumi suna tarayya a abu ɗaya, wato dukansu Ubangiji ne yake ba su ganin gari.
14
Idan sarki yana yi wa talakawa shari'ar gaskiya, zai daɗe yana mulki.
15
Horo da tsautawa suna ba da hikima, amma yaron da aka sangarta zai jawo wa mahaifiyarsa kunya.
16
Sa'ad da mugaye suke mulki, laifofi suka ƙaru, amma adalai za su ga faɗuwar waɗannan mutane.
17
Ka hori ɗanka zai daɗaɗa maka rai, ya kuma faranta maka zuciya.
18
Inda ba a bin faɗar Allah, jama'a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah.
19
Bara ba ya horuwa ta wurin magana kawai, gama ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
20
Ka ga mutum mai garajen yin magana? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
21
Baran da aka shagwaɓa tun yana yaro, a ƙarshe zai ɗauki kansa tankar magājin gida.
22
Mutum mai saurin fushi yakan ta da faɗa, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa.
23
Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.
24
Abokin ɓarawo mugun maƙiyin kansa ne, yana jinsa yana ta rantsuwa, amma ba zai ce kome ba.
25
Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a ɗaukaka shi.
26
Mutane da yawa sukan nemi farin jini daga wurin mai mulki, amma Ubangiji ne yake yi wa mutum adalci.
27
Mutum marar gaskiya abin ƙyama ne ga adali, adali kuma abin ƙyama ne ga mugun.
← Chapter 28
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 30 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31