bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Proverbs 9
Proverbs 9
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 8
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 10 →
1
Hikima ta gina gidanta, ta yi masa ginshiƙai bakwai.
2
Ta sa an yanka dabba don biki, ta gauraya ruwan inabi da kayan yaji, ta shirya tebur.
3
Ta aiki barorinta 'yan mata su je su hau wuri mafi tsayi a birni su yi kira.
4
“Ku shigo, ku jahilai!” Ga dolo kuwa ta ce,
5
“Zo ka ci abincina ka sha ruwan inabin da na gauraya.
6
Ka rabu da ƙungiyar jahilai, ka rayu, ka bi hanyar ilimi.”
7
Idan ka kwaɓi mai fāriya, za ka gamu da cin mutunci, idan ka tsauta wa mugu, kai ne za ka cutu.
8
Faufau kada ka kuskura ka kwaɓi mai fāriya, zai ƙi ka saboda wannan, amma idan ka kwaɓi mai hikima zai girmama ka.
9
Dukan abin da ka faɗa wa mutum mai hikima, zai ƙara masa hikima. Dukan abin da ka faɗa wa adali zai ƙara masa ilimi.
10
Domin ka zama mai hikima dole ka fara da tsoron Ubangiji. Idan ka san Mai Tsarki, ka sami ganewa.
11
Hikima za ta ƙara shekarunka.
12
Kai ne da riba in ka sami hikima. Kai za ka sha hasara in ka ƙi ta.
13
Wawanci kamar mace ce mai kwakwazo, jahila, marar kunya.
14
Takan zauna a ƙofar gidanta, ko a wurin da ya fi duka bisa a cikin gari.
15
Takan yi ta kiran masu wucewa waɗanda hankalinsu yake a kan ayyukansu, ta ce,
16
“Ku shigo, ku jahilai!” Takan ce wa dolo,
17
“Ruwan da aka sata ya fi daɗi, haka nan kuma abincin da ake satar ya fi daɗi.”
18
Waɗanda suka fāɗa a hannunta ba su sani mutuwa za su yi ba, waɗanda suka riga sun shiga kuwa suna can sun nutse cikin lahira.
← Chapter 8
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 10 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31