bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Proverbs 18
Proverbs 18
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 17
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 19 →
1
Mutumin da ya kula da kansa kaɗai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya faɗi maganar da take daidai ba zai yarda ba.
2
Wawa bai kula ba, ko ya fahimci abu, ko bai fahimta ba. Abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya nuna kuzarinsa.
3
Zunubi da kunya a tattare suke. Idan ka yar da mutuncinka za ka sha ba'a a maimakonsa.
4
Harshen ɗan adam yana iya zama shi ne asalin hikima mai zurfi kamar teku, sabo kamar ruwan rafi mai gudu.
5
Ba daidai ba ne a yi wa mugun mutum alheri, sa'an nan a ƙi yi wa marar laifi adalci.
6
Sa'ad da wawa ya fara jayayya, yana neman dūka ne.
7
Sa'ad da wawa ya yi magana yana lalatar da kansa ne, maganarsa tarko ce, da ita ake kama shi.
8
Ɗanɗanar jita-jita daɗi gare ta, mukan ƙosa mu haɗiye ta.
9
Rago yana daidai da mutumin da yake lalatar da abubuwa.
10
Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.
11
Attajirai suna zato dukiyarsu ita ce za ta kiyaye su kamar garuka masu tsayi da suke kewaye da birni.
12
Ba wanda za a girmama sai mai tawali'u, mutum mai girmankai kuwa yana kan hanyar hallaka.
13
Ka saurara kafin ka amsa, idan kuwa ba ka yi ba, ka zama dakiki mai bankunya.
14
Sa zuciya ga rai yakan taimaki mutum sa'ad da yake ciwo, amma idan ya karai, to, tasa ta ƙare.
15
Mutane masu basira, a ko yaushe suna da himma, a shirye kuma suke domin su koya.
16
Kana so ka sadu da babban mutum? Ka kai masa kyauta, za ka gan shi a sawwaƙe.
17
Wanda ya fara mai da magana a majalisa yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai abokin shari'arsa ya mai da tasa maganar tukuna.
18
Idan mutum biyu ƙarfafa suna jayayya da juna a gaban shari'a, kuri'a a asirce kaɗai take iya daidaita tsakaninsu.
19
Ɗan'uwan da ya ji haushinka zai gagare ka, idan ka yi faɗa da shi zai rufe maka ƙofarsa.
20
Bisa ga sakamakon hurcinka haka za ka rayu.
21
Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.
22
Idan ka sami mace ka sami abu mai kyau, wannan alheri ne wanda Ubangiji ya yi maka.
23
Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.
24
Waɗansu abokai ba su sukan ɗore ba, amma waɗansu abokai sun fi 'yan'uwa aminci.
← Chapter 17
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 19 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31