bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Proverbs 20
Proverbs 20
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 21 →
1
Ruwan inabi da barasa sukan sa ka ka yi ta tā da murya, ka zama wawa. Wauta ce mutum ya bugu.
2
Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.
3
Kowane wawa yakan fara yin jayayya, abin da ya fi daraja shi ne ka fita ka ware kanka.
4
Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.
5
Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.
6
Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.
7
'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.
8
Sarkin da yake yin shari'a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.
9
Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?
10
Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.
11
Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.
12
Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.
13
Idan barci ne sana'arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka sami wadataccen abinci.
14
Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fāriya a kan ya iya ciniki.
15
In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu'ulu'ai tamani.
16
Sai wawa kaɗai yake ɗaukar lamunin biyan basusuwan da baƙo ya ci, ya kamata a karɓi dukiyarsa jingina.
17
Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.
18
Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.
19
Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.
20
Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.
21
Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, amfaninta kaɗan ne.
22
Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.
23
Ubangiji yana ƙin waɗanda suke awo da ma'aunin algus.
24
Ubangiji ya ƙayyade hanyoyinmu, ta ƙaƙa wani zai ce ya fahimci rai?
25
Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa'adi za ka miƙa wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da na sani nan gaba.
26
Sarki mai hikima zai bincika ya gane waɗanda suke aikata mugunta, ya hukunta su ba tausayi.
27
Ubangiji ne ya ba mu hankali da lamiri, ba za mu iya ɓoye masa ba.
28
Sarki zai zauna dafa'an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci, da adalci, da daidaita.
29
Ƙarfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce.
30
Wani lokaci sai mun sha wuya muke sāke hanyoyinmu.
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 21 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31