bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Jeremiah 12
Jeremiah 12
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 11
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 13 →
1
Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?
2
Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa, Suna girma, suna kuma ba da 'ya'ya, Sunanka na a cikin bakinsu, amma kana nesa da zuciyarsu.
3
Amma kai, ya Ubangiji, kana sane da ni, kana ganina, Kai kanka kake gwada tunanina. Ka jawo su kamar tumaki zuwa mayanka, Ka ware su domin ranar yanka.
4
Sai yaushe ƙasar za ta daina makoki, Ciyawar kowace saura kuma ta daina yin yaushi? Saboda muguntar mazaunan ƙasar ne dabbobi da tsuntsaye suka ƙare, Domin mutanen suna cewa, “Ba zai ga ƙarshenmu ba.”
5
Ubangiji ya ce, “Idan kai da mutane kun yi tseren ƙafa sun gajiyar da kai, Yaya za ka iya gāsa da dawakai? Idan ka fāɗi a lafiyayyiyar ƙasa, Ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?
6
Gama har da 'yan'uwanka da gidan mahaifinka, Sun ci amanarka, Suna binka da kuka, Kada ka gaskata su, Ko da yake suna faɗa maka maganganu masu daɗi.”
7
Ubangiji ya ce, “Na bar jama'ata. Na rabu da gādona, Na ba da wanda raina yake ƙauna a hannun maƙiyansa.
8
Abin gādona ya zama mini kamar zaki a cikin kurmi, Ya ta da murya gāba da ni, Domin haka na ƙi shi.
9
Ashe, abin gadon nan nawa ya zama dabbare-dabbaren tsuntsun nan ne mai cin nama? Tsuntsaye masu cin nama sun kewaye shi? Tafi, ka tattaro namomin jeji, Ka kawo su su ci.
10
Makiyaya da yawa sun lalatar da gonar inabina. Sun tattake nawa rabo, Sun mai da nawa kyakkyawan rabo kufai da hamada.
11
Sun maishe shi kufai, ba kowa, Yana makoki a gare ni, Ƙasar duka an maishe ta kufai, Amma ba wanda zuciyarsa ta damu a kan wannan.
12
A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.
13
Sun shuka alkama, sun girbe ƙayayuwa, Sun gajiyar da kansu, amma ba su amfana da kome ba. Za su sha kunya saboda abin da suke girbe, Saboda zafin fushin Ubangiji.”
14
Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.
15
Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.
16
Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al'amuran jama'ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, ‘Da zatin Ubangiji,’ kamar yadda suka koya wa jama'ata yin rantsuwa da Ba'al, sa'an nan za a gina su a tsakiyar jama'ata.
17
Amma idan wata al'umma za ta ƙi kasa kunne, to, sai in tumɓuke ta ɗungum, in hallaka ta, in ji Ubangiji.”
← Chapter 11
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 13 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52