bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Jeremiah 20
Jeremiah 20
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 21 →
1
Sa'ad da Fashur, firist, ɗan Immer, shugaban Haikalin Ubangiji ya ji Irmiya yana annabci a kan waɗannan abubuwa,
2
sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka, aka kuma sa shi cikin turu a ƙofar Biliyaminu, a Haikalin Ubangiji.
3
Kashegari sa'ad da Fashur ya fitar da Irmiya daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashur ba, amma ya ba ka suna Magormissabib, wato razana ta kowace fuska.
4
Haka Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan maishe ka abin tsoro ga kai kanka, da dukan abokanka. Abokan gābansu za su kashe su da takobi a kan idonka. Zan ba da dukan Yahuza a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai kwashe waɗansu ya kai bautar talala a Babila, ya kuma kashe waɗansu da takobi.
5
Banda haka kuma zan ba da dukan dukiyar wannan birni, da dukan ribarsa, da dukan abubuwa masu tamani, da dukan dukiyar sarakunan Yahuza, ga abokan gābansu, waɗanda za su washe su, su kama su, su kai Babila.
6
Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda suke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.’ ”
7
“Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu, Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni. Na zama abin dariya dukan yini, Kowa yana ta yi mini ba'a.
8
Duk lokacin da zan yi magana, Nakan ta da murya in yi magana da ƙarfi cewa, ‘Hargitsi da hallakarwa!’ Gama saboda maganar Ubangiji na zama abin zargi, Da abin ba'a dukan yini.
9
Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangiji ba, Ban zan ƙara yin magana da sunansa ba,’ Sai in ji damuwa a zuciyata, An kulle ta a ƙasusuwana, Na gaji da danne ta a cikina, Ba zan iya jurewa ba.
10
Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’
11
Amma Ubangiji kana tare da ni Kamar jarumi mai bantsoro, Don haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe, Ba za su rinjaye ni ba. Za su sha kunya ƙwarai, Gama ba za su yi nasara ba. Ba za a manta da su ba.
12
Ya Ubangiji Mai Runduna, mai gwada adali, Mai ganin zuciya duk da tunani, Ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, Gama a gare ka nake kawo ƙarata.”
13
Ku raira waƙa ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji! Gama ya kuɓutar da ran mabukaci daga hannun mugaye.
14
La'ananniya ce ranar da aka haife ni, Kada ranar da uwata ta haife ni ta yi albarka!
15
La'ananne ne mutum da ya kai wa mahaifina labari Cewa, “An haifa maka ɗa,” don ya sa shi farin ciki.
16
Bari wannan mutum ya zama kamar biranen da Ubangiji ya kaɓantar ba tausayi. Bari ya ji kuka da safe, Da rana kuma ya ji gangamin yaƙi,
17
Domin bai kashe ni tun ina ciki ba. Da ma cikin uwata ya zama mini kabari, In yi ta kwanciya a ciki har abada.
18
Me ya sa na fito daga cikin mahaifa, Don in ga wahala da baƙin ciki, Don kwanakin raina su ƙare da kunya?
← Chapter 19
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 21 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52